NLC: Muhimman Abubuwan da Aka Tattake Wuri a Kansu a Taron Mafi Ƙarancin Albashi

NLC: Muhimman Abubuwan da Aka Tattake Wuri a Kansu a Taron Mafi Ƙarancin Albashi

  • Ministar kwadago ta bayyana abubuwan da aka tattauna a taron kwamitin mafi ƙarancin albashi ranar Laraba, 5 ga watan Yuni
  • Tun farko dai gwamnatin tarayya ta tabbatarwa ƴan kwadago cewa a shirye take ta ƙara wani abu a kan tayin N60,000 da ta yi a baya
  • Duk da ba a kammala tattaunawa kan sabon mafi ƙarancin albashin ba, a taron jiya, Nkeiruka Onyejeocha ta ce saura ƙiris a cimma matsaya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce tattaunawa ta yi nisa da ƴan kwadago domin cimma matsaya kan sabon mafi ƙarancin albashi a Najeriya

Karamar ministar kwadago da samar da ayyukan yi, Nkeiruka Onyejeocha ta sanar da haka bayan fitowa daga taron kwamitin mafi ƙarancin albashi ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Mafi karancin albashi: Dalilin gaza cimma matsaya tsakanin gwamnati da 'yan kwadago

Bola Ahmed Tinubu.
Ministar kwadago ta ce an kusa karkare batun mafi ƙarancin albashi Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Ana shirin samun mafi karancin albashi

Ministar ta ce nan ba da jimawa ba za a samu matsaya da ƴan kwadago kan batun ƙarin albashin, wanda ya jawo suka yi yajin aikin kwana ɗaya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Onyejeocha ta wallafa a shafinta na manhajar X cewa suna ci gaba da tattaunawa kan sabon mafi ƙarancin albashi kuma sun zo matakin ƙarshe.

Gwamnati ta gana da NLC kan albashi

A cewarta, kwamitin da aka kafa ya samu zama ranar Laraba kuma wakilan kowane ɓangare sun halarta, an tattauna muhimman batutuwa a taron.

"Ana ci gaba da tattake wuri, kwamitin mafi ƙarancin albashi ya zauna yau domin warware wasu muhimman batutuwa.
"Babu wata matsala daga gare mu kuma ina da yaƙinin za a samu maslaha da wuri fiye da yadda ake tsammani.
"Muna da tarin abubuwan masu muhimmanci a gabanmu waɗanda za su inganta rayuwar al'ummar ƙasar nan."

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu, ƴan ƙwadago da kamfanoni sun shiga ganawa a Abuja

Abubuwan da suke damun Najeriya

Idan ba ku manta ba, tun da daɗewa manyan ƙungiyoyin kwadago NLC da TUC suka koka kan tsadar rayuwa da wahalhalun da al'umma suka wayi gari a ciki.

Sun buƙaci gwamnati ta magance matsalolin da ke damun mutane kamar rashin aikin yi, gidaje, rashin tsaro da kuma tsadar kayayyakin masarufi a kasar nan.

Kotu ta kwace kadarorin Emefiele

A wani labarin na daban, kotu ta bayar da umarnin wucin gadi na kwace wasu manyan kadarorin maƙudan kuɗi na tsohon gwamnan CBN, Godwin Emefiele

Mai shari'a Chukwujekwu Aneke na babbar kotun tarayya mai zama a Legas ne ya bayar da wannan umarnin ranar Laraba, 5 ga watan Yuni.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262