Gwamnatin Tinubu, Ƴan Kwadago da Kamfanoni Sun Shiga Ganawa a Abuja

Gwamnatin Tinubu, Ƴan Kwadago da Kamfanoni Sun Shiga Ganawa a Abuja

  • Gwamnatin tarayya, ƙungiyoyin kwadago da kamfanoni masu zaman kansu sun sake shiga taro kan mafi ƙarancin albashin ma'aikata
  • Rahoto ya nuna cewa wakilan gwamnatin tarayya a taron sun haɗa da ministan kuɗi, ministan kasafi da tsare-tsaren ƙasa da ministan kwaɗago
  • Shugabannin NLC da na TUC sun halarci zaman na yau Laraba, 5 ga watan Yuni, 2024 a madadin ɗaukacin ma'aikatan Najeriya

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Rahotanni sun nuna cewa kwamitin mafi ƙarancin albashi ya ci gaba da zaman tattaunawa a Otal na Nicon Luxury Hotel da ke Abuja ranar Laraba.

Kwamitin mai kunshe ɓangarori uku, gwamnatin tarayya, kamfanoni masu zaman kansu da ƴan kwadago, zai ci gaba tattaunawa kan sabon mafi ƙarancin albashi.

Kara karanta wannan

Tsohon gwamnan CBN ya shiga tasku, kotu ta ƙwace manyan kadarorinsa na N11.1bn

Yan kwadago da Bola Tinubu.
Kwamitin mafi ƙarancin albashi ya koma teburin tattaunawa da ƴan kwadago Hoto: NLC, Dolusegun
Asali: Facebook

Kwadago: Jerin wakilan gwamnatin Tinubu

Waɗanda suka wakilci gwamnatin tarayya sun haɗa da ministan kuɗi, Wale Edun, ministan kasafi da tsare-tsaren kasa, Atiku Bagudu da ministan kwadago, Nkeiruka Onyejeocha.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wakilan sakataren gwamnatin tarayya da shugabar ma'aikata ta kasa sun halarci taron yau Laraba, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

A ɗaya ɓangaren kuma shugaban kungiyar kwadago (NLC), Joe Ajaero da takwaransa na TUC, Festus Osifo, suna wurin a madadin ma'aikatan Najeriya.

Gwamnoni sun halarci taron 'yan kwadago?

Darakta Janar na kungiyar gwamnonin Najeriya (NGF), Abdulateef Shittu ya halarci zaman wanda za a lalubo matsaya kan sabon mafi ƙarancin albashi.

Sai dai har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton, babu gwamnan da aka gani a wurin taron na yau Laraba a Abuja.

Wannan na zuwa ne sa'o'i 24 bayan ƴan kwadago sun janye yajin aikin da suka fara, wanda ya tsaida dukkan harkokin tattalin arziki a ƙasar nan.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya shiga muhimmin taro kan mafi karancin albashi, bayanai sun fito

Amma gwamnatin tarayya ta yi alƙawarin cewa za ta ƙara wani abu a kan N60,000 da ta gabatar a matsayin mafi ƙarancin albashi, Channels tv ta rahoto.

Kotu ta kwace kadarorin Emefiele

A wani rahoton kuma kotu ta bayar da umarnin wucin gadi na kwace wasu manyan kadarorin maƙudan kuɗi na tsohon gwamnan CBN, Godwin Emefiele.

Mai shari'a Chukwujekwu Aneke na babbar kotun tarayya mai zama a Legas ne ya bayar da wannan umarnin ranar Laraba, 5 ga watan Yuni.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel