Tsohon Gwamnan CBN Ya Shiga Tasku, Kotu Ta Kwace Manyan Kadarorinsa Na N11.1bn
- Kotu ta bayar da umarnin wucin gadi na kwace wasu manyan kadarorin maƙudan kuɗi na tsohon gwamnan CBN, Godwin Emefiele
- Mai shari'a Chukwujekwu Aneke na babbar kotun tarayya mai zama a Legas ne ya bayar da wannan umarnin ranar Laraba, 5 ga watan Yuni
- Tun farko hukumar yaƙi da rashawa EFCC ta buƙaci kotun ta kwace kadarorin saboda ana tuhumar da kuɗin sata ya mallake su
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Lagos - Babbar kotun tarayya mai zama a jihar Legas ta kwace kadarorin N11.1bn na tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele.
Kotun ta bai wa gwamnatin tarayya umarnin wucin gadi ta karɓe kadarorin da suka kai darajar N11,140,000,000 na Emefiele, tsohon gwamnan CBN.
Alkali ya karbe dukiyar Godwin Emefiele
Mai shari'a Chukwujekwu Aneke ya bayar da wannan umarni a zaman shari'a na yau Laraba, 5 ga watan Yuni, 2024, kamar yadda The Cable ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Alkalin ya amince da ƙwace manyan kadarorin biliyoyin Naira na Emefiele ne bayan lauyan hukumar EFCC, Rotimi Oyedepo, ya shigar da buƙatar hakan.
Meyasa kotu ta kwace kadarorin?
Babban Lauyan ya shaidawa kotun cewa ana zargin Emefiele da amfani da kuɗin da ya wawura wajen sayan manyan kadarori, kuma jawo wasu ya sa su wakilce shi.
An ce wadannan kadarorin da aka kwace suna cikin manyan Unguwannin masu kuɗi a babban birnin tarayya (FCT), Abuja, Sahara Reporters ta ruwaito.
EFCC ta kuma ambaci sunayen wasu jami’an CBN guda uku, Obayemi Oluwaseun Teben, Akomolafe Adebayo, da Olubunmi Makinde, ta ce sun taimakawa Emefiele.
Kotu ta umarci EFCC ta buga labarin
Bayan kwace kadarorin, kotun ta umarci EFCC ta buga labarin a jaridu domin neman masu sayen kadarorin gabanin a gama kwace su gaba ɗaya.
Mai shari'a Aneke ya dage ci gaba da sauraron karar zuwa ranar 21 ga watan Yuni domin yanke hukunci kan bukatar kwace su har abada daga hannun Emefiele.
Daraktan CBN ya tona asirin Emefiele
A wani rahoton kuma hukumar EFCC ta gabatar da shaida a gaban babbar kotun Abuja a shari'ar tsohon gwamnan babban banki CBN, Godwin Emefiele.
Tsohon daraktan sashin ayyuka na CBN, Ahmed Umar, ya faɗi yadda Emefiele ya aiwatar da tsarin sauya fasalin Naira ba tare da amincewa ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng