APC Ta Zargi Gwamna Fubara da Kaddamar da Ayyukan da Wike Ya Yi a Matsayin Nasa

APC Ta Zargi Gwamna Fubara da Kaddamar da Ayyukan da Wike Ya Yi a Matsayin Nasa

  • Gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara ya kaddamar da wasu manyan ayyuka a lokacin da ya cika shekara a kan karaga
  • Sai dai jam'iyyar APC a jihar ta yi inkarin ayyukan, inda ta ce ba gwamna Fubara ba ne ya yi su cikin shekarar da ya yi a mulki
  • A nata bangaren, gwamnatin jihar Ribas karkashin gwamna Fubara ta mayar da martani mai zafi ga jam'iyyar APC a kan lamarin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Rivers - An samu musayar yawu tsakanin jam'iyyar APC da gwamnatin jihar Ribas kan ayyukan da gwamna Siminalayi Fubara ya kaddamar.

Gwamna Fubara ya kaddamar da ayyukan ne yayin bikin cikar shi shekara daya kan karagar mulki.

Kara karanta wannan

APC ta yi hannun riga da wani tsohon gwamna, ta cire shi daga jagororin jam'iyya

Gwamna Fubara
APC ta zargi gwamna Fubara da bude ayyukan da ba nashi ba. Hoto: Sir Siminalayi Fubara
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ruwaito APC na cewa tsohon gwamnan jihar, Nyesom Wike ya fara ayyukan ba gwamna Fubara ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ayyukan da gwamna Fubara ya kaddamar

A lokacin da ya yi bikin cika shekara daya kan karaga, gwamna Fubara ya kaddamar da ayyuka a jihar Ribas ciki har da manyan tituna.

Cikin titunan da ya kaddamar akwai hanyar Etewo Eleme da hanyar Andoni Ogoni Obobo da hanyar Kalabari a jihar Ribas.

APC ta zargi Fubara kan ayyuka

Amma sai dai jam'iyyar APC a jihar ta yi martani inda ta ce ba gwamna Fubara ba ne ya fara ayyukan da kansa, rahoton Tribune.

Ta ce dukkanin ayyukan tsohon gwamnan jihar, Nyesom Wike ne ya fara su a lokacin da yake gwamnan jihar.

Fubara: Gwamnan Ribas ya yi martani ga APC

Kara karanta wannan

Gwamnatin Gombe za ta yi titin da kilomita 1 zai lakume sama da Naira biliyan 1

Sai dai a na shi bangaren, gwamna Siminalayi Fubara ya ce babu kamshin gaskiya a cikin maganar da APC ta yi.

Kwamishinan yada labarai na jihar Ribas, Barista Joseph Johnson ya ce gwamna Fubara ne ya fara ayyukan kuma ya kammala su.

Har ila yau, kwamishinan ya ce akwai sauran ayyukan da gwamna Fubara ya fara amma nan gaba za a karasa su da yardar Allah.

Gwamna Fubara ya koka kan Wike

A wani rahoton, kun ji cewa yayin murnar cika shekara daya a kan mulki, gwamnan jihar Ribas Siminalayi Fubara ya bayyana yadda aka bar masa tarin bashi.

Har ila yau, Fubara ya kuma bayyana dalilin da yasa tsohon gwamna Nyesom Wike ya fara yakarsa tun wata uku da zamansa gwamna.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Online view pixel