Ana Fargabar Masu Kwacen Waya Sun Kashe Sojan Najeriya, Tsohon Sanata Ya Magantu

Ana Fargabar Masu Kwacen Waya Sun Kashe Sojan Najeriya, Tsohon Sanata Ya Magantu

  • Wasu ‘yan daba da suka kware wajen satar waya da sauran laifuka sun kashe wani jami’in soja mai suna Laftanar I.M Abubakar
  • An ruwaito cewa masu kwacen wayar sun kashe sojan ne a Unguwan Sarki da ke cikin birnin Kaduna a hanyarsa ta komawa gida
  • Tsohon sanatan Kaduna, Shehu Sani ya yi Allah wadai da wannan aika-aika tare da yin kira ga jami'an tsaro da su kamo masu laifin

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Kaduna - Rahotanni sun bayyana cewa wasu ‘yan daba da suka kware wajen satar waya da sauran laifuka sun kashe wani jami’in soja mai suna Laftanar I.M Abubakar.

An ruwaito cewa masu kwacen wayar sun kashe sojan ne a Unguwan Sarki da ke cikin birnin Kaduna a cikin makon nan.

Kara karanta wannan

Miyagun 'yan bindiga sun kashe ɗan majalisar yanki da shugaban matasa

Shehu Sani ya yi magana kan kashe wani soja a Kaduna
Kaduna: Masu kwacen waya sun kashe wani sojan Najeriya. Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Shahararren masani kan yaki da tada kayar baya kuma mai sharhi kan harkokin tsaro a tafkin Chadi, Zagazola Makama ya bayyana hakan a shafinsa na Twitter.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Masu kwacen waya sun kashe soja

Makama ya bayyana Abubakar a matsayin jami'in soja mai hazaka wanda aka kashe a hanyarsa ta komawa gida a Kaduna.

Sanarwar Makama na cewa:

“Masu satar waya sun kashe wani matashin jami'in soja mai hazaka, Laftanar I.M Abubakar (Isa) a kan hanyarsa ta komawa gida a Unguwan Sarki, Kaduna.
"Muna addu'ar Allah ya jikan sa da Rahama, ya sa ya huta."

Kisan soja: Shehu Sani ya yi Allah wadai

Da yake tsokaci kan kashe Laftanar I.M Abubakar, tsohon sanatan Kaduna, Shehu Sani ya yi tir da wannan aika-aika da masu kwacen wayar suka yi.

Kamar yadda ya wallafa a shafinsa na X (Twitter), Shehu Sani ya ce:

Kara karanta wannan

Kaduna: An shiga tashin hankali, wata amarya ta datse mazakutar angonta

"Rahotan kashe Laftanar Abubakar da wasu barayin waya suka yi a Unguwar Sarki da ke cikin birnin Kaduna, abin takaici ne kuma abin Allah wadai.
Yawaitar rahotannin hare-hare da ke da alaka da kwacen waya a birane ya fara zama abin tsoro. Dole ne hukumomin tsaro su kamo wadanda suka aikata wannan aika aikar."

Shehu Sani ya mika sakon ta'aziyya ga iyalan marigayi Laftanar I.M Abubakar tare da addu'ar Allah ya jikan sa da Rahama.

Amarya ta datse mazakutar ango a Kaduna

A wani labarin, mun ruwaito cewa wata amarya mai suna Habiba Ibrahim ta sa wuka mai kaifi ta yanke mazakutar angonta Salisu Idris a garin Kudan, jihar Kaduna.

An gano cewa ma'auratan sun yi auren soyayya ne kuma duka-duka watannin su biyar da yin auren a lokacin da Habiba ta yi wannan aika-aikar sa'ilin da Salisu ke barci.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel