Yajin Aiki: NLC Ta Fadi Karin Albashin da Take Bukata Gwamnati Ta Yi a Kan N60,000

Yajin Aiki: NLC Ta Fadi Karin Albashin da Take Bukata Gwamnati Ta Yi a Kan N60,000

  • A ranar Talata kungiyar kwadago ta janye yajin aiki na mako daya domin cigaba da tattaunawa da gwamnatin tarayya
  • Kungiyar kwadago ta yi karin haske kan kudin da ta ke buƙata gwamnati ta kara domin janye yajin aikin baki daya
  • Gwamantin ta yi alkawarin dawo da mafi ƙarancin albashi N60,000 ita kuma kungiyar kwadago da dage sai N494,000

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Nigeria - Kungiyar kwadago ta yi magana kan mafi ƙarancin albashi kwana ɗaya bayan janye yajin aiki na mako guda.

Kungiyar tace ta janye yajin aikin ne domin ba gwamnatin tarayya damar samun natsuwa da cigaba da tattaunawa

Yan kwadago
Yan kwadago sun fadi karin da suke nema wajen gwamnati. Hoto: @NLCHeadquaters
Asali: Twitter

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa shugaban kungiyar TUC, Festus Osifo ne ya yi jawabin a lokacin hira da 'yan jarida.

Kara karanta wannan

Kungiyar ƙwadago ta janye yajin aiki, ta ba gwamnatin tarayya wa'adin mako 1

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

NLC ta bukaci karin albashi mai yawa

Kungiyar kwadago ta janye yajin aiki ne bayan cimma matsaya kan cewa gwamnati za ta mayar da mafi ƙarancin albashi sama da N60,000.

Amma sai dai shugaban TUC, Festus Osifo ya ce kungiyar ba za ta amince da karin kudi kaɗan kan N60,000 ba.

Albashin nawa TUC ke buƙata a wata?

Festus Osifo bai ayyana kudin da suke so gwamnati ta kara ba, amma ya ce ya kamata ta nuna ta damu da ma'aikata, ta yi kari mai gwaɓi.

Sai dai ya tabbatar da cewa ƙarin kudi kamar N3,000 da makamancinsa ba zai saka kungiyar ta janye yajin aikin baki daya ba.

Ya ce dole kudin da za a kara ya kai darajar N30,000 a shekarar 2019 ko kuma N18,000 a shekarar 2014, rahoton Daily Post.

A ranar Litinin, 3 ga watan Yuni ne kungiyar kwadago ta shiga yajin aiki kan neman karin mafi ƙarancin albashi a Najeriya.

Kara karanta wannan

Gwamnati ta bayyana yadda yajin aikin 'yan NLC zai kara jefa al'umma a wahala

NLC ta dakatar da shari'a a Abuja

A wani rahoton, kun ji cewa yajin aikin yan kwadago ya tsayar da harkokin shari'a cak a birnin tarayya Abuja inda aka rufe kotuna baki daya.

Rahotanni sun tabbatar da cewa ma'aikatan shari'a reshen Abuja sun hana alkalai, lauyoyi da masu shigar da kara da 'yan jarida shiga kotuna a birnin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Online view pixel