Mutane 8 Sun Mutu Yayin da Aka Yi Asarar Dukiyar da Ta Kai N31.6m a Jihar Kano

Mutane 8 Sun Mutu Yayin da Aka Yi Asarar Dukiyar da Ta Kai N31.6m a Jihar Kano

  • An rasa rayukan mutum takwas kuma kadarorin da suka kai na N31.6m sun salwanta a ibtila'in gobara a jihar Kano cikin watan Mayu
  • Mai magana da yawun hukumar kashe gobara ta jihar, Saminu Yusif Abdullahi ne ya faɗi haka da yake jawabi kan ayyukan hukumar a watan jiya
  • Jami'in ya shawarci mutane su riƙa kokarin kai ɗauki idan wuta ta kama, sannan ya gargaɗi direbobi su yi tuki da taka tsan-tsan

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kano - Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta bayyana matsalolin tashin gobarar da ta fuskanta da asarar da mutane suka yi cikin watan Mayun da ya gabata a jihar.

Hukumar ta ce ibtila'in gobara daban-daban da suka faru sun yi ajalin mutane takwas tare da lalata kadarorin da kudinsu ya kai N31,650,700 a watan Mayu.

Kara karanta wannan

An cafke ɗan majalisa da basarake kan zargin daukar nauyin ta'addanci a Zamfara

Taswirar jihar Kano.
Gobara ta zama ajalin mutum 8 a jihar Kano a watan Mayu, 2024
Asali: Original

Mai magana da yawun hukumar na jihar Kano, Saminu Yusif Abdullahi, shi ne ya bayyana haka a ranar Talata, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gobarar da ta faru a Kano

Ya ce jami'an kwana-kwana sun kai ɗauki bayan samun kiran gaggawa daban-daban a tashohin ƴan kwana-kwana 29 a watan Mayun 2024.

Saminu ya ce kira-kirayen da suka samu sun haɗa da kawo rahoton tashin wuta guda 51, na neman ɗauki 13 da kuma sanarwar ƙarya guda shida.

"Ƙiyasin kadarorin da gobara ta lalata a cikin watan Mayu sun kai N31,650,700, yayin da ƙiyasin kimar kadarorin da jami'an kashe gobara na jihar suka ceto ya kai N98,700,000.
"An rasa rayukan mutane takwas yayin da jami'ai suka samu nasarar ceto mutum 10."

Hukumar ta gargaɗi mutanen Kano

Abdullahi ya bukaci ɗaukacin al'umma da su yi taka-tsan-tsan wajen ƙoƙarin ƙai ɗauki da kashe gobara domin daƙile barna kafin isowar jami'an hukumar.

Kara karanta wannan

Shaguna sun kone bayan gobara ta tashi a babbar kasuwar Katako

Ya kuma shawarci masu ababen hawa da su rika tuƙi a hankali tare da bin dokokin hanya domin gujewa hadurra.

Kano: Hisbah ta kama G-Fresh

A wani rahoton na daban, an ji hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama fitaccen ɗan TikTok , G-Fresh Al'ameen saboda zargin yiwa Kur'ani izgili.

Babban daraktan Hisbah na jihar, Mallam Abba Sufi ne ya tabbatar da kama G-Fresh ga manema labarai a ranar Lahadi da ta gabata.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262