Dahiru Bauchi Ya Yi Biris da Sanusi II, Ya Yi Mubaya’a Ga Aminu Bayero
- Iyalan babban malamin addinin Musulunci, Sheikh Dahiru Usman Bauchi sun kai ziyara ga mai martaba Aminu Ado Bayero
- Sheikh Ibrahim Sheikh Dahiru Usman Bauchi ne ya jagoranci tawagar zuwa gidan Sarkin Kano da ke unguwar Nasarawa
- Ziyarar ta zo ne kwana ɗaya bayan wasu daga cikin iyalan shehin sun ziyarci mai martaba Muhammadu Sanusi II a fadar sa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Yayin da aka gaza cimma matsaya kan sarautar Kano, al'umma na cigaba da nuna goyon baya ga ɓangarorin Sanusi II da Aminu Ado Bayero.
Iyalan Sheikh Dahiru Usman Bauchi sun ziyarci mai martaba Aminu Ado Bayero domin mara masa baya.
A wani bidiyo da Gawuna Online suka wallafa a shafin Facebook Sheikh Ibrahim Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya ce sun kai ziyarar ne a madadin Sheikh Dahiru Usman Bauchi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dalilin ziyartar Aminu Ado Bayero
A cikin bidiyon, Sheikh Ibrahim Dahiru Bauchi ya ce sun kai ziyara ga Aminu Ado Bayero ne domin masa jaje kan abin da ya faru.
A wani bidiyon da Masarautar Kano ta wallafa a Facebook kuma Legit ta ga Ibrahim Dahiru Bauchi ya sanyawa Aminu Ado Bayero alkyabba domin nuna mubaya'a a madadin Shehi.
Matsayar Dahiru Bauchi kan sarautar Kano
Sheikh Ibrahim Dahiru Bauchi ya bayyana cewa Shehu Dahiru Bauchi yana kan matsayarsa ta farko kan yarda da wanda yake kan mulki tun asali.
Ya kuma kara da cewa duk da haka Shehi ya ce a jira shari'a ta zartar da hukuncin karshe a kan dambarwar.
'Ya'yan Dahiru Bauchi sun ziyarci Sanusi II
Ibrahim Dahiru Bauchi ya ce wasu daga cikin 'ya'yan Shehi da suka ziyarci Sanusi II ba Shehi ba ne ya tura su.
Ya tabbatar da cewa dama suna da alaka ta abota tsakaninsu da Muhammadu Sanusi II saboda haka suka ziyarce shi.
TCN ta gyara wuta a Arewa
A wani rahoton, kun ji cewa bayan shafe kwanaki sama da 50 babu wuta a yankin Arewa maso gabashin Najeriya, hukumomi sun yi albishir ga mazauna yankin.
Hukuma mai rarraba wutar lantarki ta kasa (TCN) ta sanar da kammala gyaran wutar lantarki a yankin wanda hakan zai ba su damar samun haske bayan shiga duhu na wani lokaci.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng