Rikicin Masarauta: Gwamna Abba Ya Nemi Muhimmiyar Bukata Wajen Lauyoyin Najeriya
- Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya buƙaci ƙungiyar lauyoyin Najeriya da ta samar da mafita kan rikicin masarautar jihar
- Gwamnan ya yi wannan kiran ne kan hukunce-hukunce masu cin karo da juna da alƙalai ke yankewa dangane da rikicin masarautar waɗanda suka haifar da ruɗani
- Gwamna Abba ya kuma buƙaci lauyoyin da su riƙa faɗin gaskiya komai ɗacinta ga abokan hulɗarsu maimakon yin abin da ya saɓa doka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kano - Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi kira ga ƙungiyar lauyoyin Najeriya (NBA) kan hukunce-hukunce masu cin karo juna da alƙalai ke yankewa kan rikicin masarautar Kano.
Gwamnan ya buƙaci ƙungiƴar lauyoyin da ta samar da mafita kan lamarin saboda ruɗanin da hakan ke haifarwa.
Wace buƙata Gwamna Abba ya nema?
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi kira a wajen wani taro na NBA a birnin Kano ranar Talata, 4 ga watan Yunin 2024, cewar rahoton jaridar The Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnan wanda sakataren gwamnatin jihar Abdullahi Bichi ya wakilce shi a wurin taron, ya shaidawa lauyoyin cewa su riƙa faɗawa abokan hulɗar su gaskiya.
Ya ce duk da gaskiya ɗaci gareta hakan yafi a ce sun yi abin da ya saɓawa doka.
Sanusi II ya yi jawabi a wajen taron NBA
A ranar Talata, ƙungiyar NBA ta gayyaci Sanusi II domin yin jawabi a taron shekara-shekara na ƙungiyar, rahoton jaridar Leadership ya tabbatar.
A nasa jawabin, Sarki Sanusi II, wanda Mahe Bashir Wali (Walin Kano) ya wakilta, ya yi maraba da mahalarta taron inda ya shaida musu cewa Kano tana da daɗaɗɗen tarihi a matsayin cibiyar al’adu da kasuwanci ta yankin Arewa.
Ya bayyana cewa taken taron, "Adalci a Najeriya: ƙalubale da gyara," na nuni da cewa adalci shi ne ƙashin bayan al'umma domin sai da adalci ake samun zaman lafiya da ci gaba.
Gwamna Abba ya samu yabo
A wani labarin kuma, kun ji cewa jam’iyyar NNPP reshen jihar Legas ta yabawa gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, bisa ƙoƙarinsa na kiyaye martabar al’adun gargajiyar jihar.
Jam'iyyar ta kuma yabawa gwamnan kan sake naɗa Muhammadu Sanusi II a matsayin Sarkin Kano bayan an tuɓe shi a lokacin gwamnatin da ta gabata.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng