'Yan Bindiga Sun Hallaka Dan Basarake Kan Auren Budurwar Shugabansu

'Yan Bindiga Sun Hallaka Dan Basarake Kan Auren Budurwar Shugabansu

  • Wasu miyagun ƴan bindiga sun shiga har gida sun hallaka ɗan Sarkin Hausawa na Janjala a ƙaramar hukumar Kagarko ta jihar Kaduna
  • Ƴan bindigan sun hallaka Safiyanu Ibrahim tare da ƙaninsa Nasiru Abubakar, ƴan kwanaki kaɗan bayan ya auri mata ta biyu
  • Bayanai sun bayyana cewa ƴan bindigan sun hallaka marigayin ne saboda ya auri budurwar shugabansu duk da gargaɗin da aka yi masa

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Bayanai sun fito kan kisan da ƴan bindiga suka yiwa ɗan Sarkin Hausawa na Janjala a ƙaramar hukumar Kagarko ta jihar Kaduna, Safiyanu Ibrahim.

Wani ɗan uwan marigayin ya yi iƙirarin cewa an harbe shi ne saboda ya dage sai ya auri mata ta biyu wacce ta kasance budurwar shugaban ƴan bindiga.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun farmaki ofishin 'yan sanda, an yi musayar wuta

'Yan bindiga sun hallaka dan Sarkin Hausawa a Kaduna
Dan Sarkin Hausawan ya kasa shugaban 'yan bindiga wajen budurwa a Kaduna Hoto: @PoliceNG
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ce a ranar Asabar, 18 ga watan Mayu, 2024, ƴan bindiga sun kai farmaki gidan Sarkin Hausawa na Janjala, inda suka harbe Safiyanu Ibrahim da kuma ƙaninsa, Nasiru Abubakar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa ƴan bindiga suka kashe ɗan Sarkin?

Wani ɗan uwansa wanda ya nemi a sakaya sunansa saboda dalilai na tsaro, ya bayyana cewa shugaban ƴan bindigan ya gargaɗi marigayin da ya ƙauracewa sabuwar amaryar tasaba ta fito daga jihar Zamfara.

Majiyar ta ci gaba da cewa, marigayi Safiyanu ya haɗu da matarsa ​​ta biyu a garin Kagarko inda suka fara soyayya, amma da shugaban ƴan bindigan, wanda saurayinta ne ya samu labari, sai ya gargaɗi Safiyanu da ya janye.

"Bayan ɗaurin auren, sai amaryar ta ƙi yarda da shi, har sai da ɗaya daga cikin abokansa ya shiga cikin lamarin, amma washegari ƴan bindigan suka zo suka kashe shi."

Kara karanta wannan

Tambuwal ya fadi dalilin da ya sa 'yan Najeriya suka tsinci kansu cikin tsadar rayuwa

"Amaryar ta bar gidan aurenta ne kwana guda bayan ƴan bindigan sun kashe mijinta, lamarin da ya sa danginsa suka shiga shakku domin har yanzu ba a san inda take ba.”

- Wata majiya

Me ƴan sanda suka ce kan lamarin?

Rundunar ƴan sandan jihar Kaduna ba ta ce komai ba kan kisan da aka yiwa ɗan Sarkin Hausawan har zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton.

Ƙoƙarin jin ta bakin kakakin rundunar ƴan sandan jihar, ASP Mansur Hassan ƴa ci tura domin ba a same shi ta waya ba.

Ƴan bindiga sun farmaki ƴan majalisa

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƴan bindiga sun farmaki tawagar 'yan majalisar dokokin jihar Benuwai a kan titin Makurɗi zuwa Gboko.

Shaidun ganau ba jiyau ba sun bayyana cewa ƴan bindigar sun kai wa ƴan majalisar hari da misalin ƙarfe 10:00 a dare a daidai kauyen Tyomu mai nisan kilomita 16 zuwa Makurdi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel