Ana Tsaka da Rigimar Sarautar Kano, Sarki Sanusi II Ya Faɗi Abin da Zai Kawo Ci Gaba a Ƙasa

Ana Tsaka da Rigimar Sarautar Kano, Sarki Sanusi II Ya Faɗi Abin da Zai Kawo Ci Gaba a Ƙasa

  • Sarki Muhammadu Sanusi II ya ja hankalin al'umma kan muhimmancin adalci idan har ana son zaman lafiya da ci gaba a ƙasa
  • Sarkin da aka mayar kan sarauta kwanan nan ya yi jawabi a wurin buɗe taron ƙungiyar lauyoyi ta ƙasa (NBA) a Kano ranar Talata
  • Gwamna Abba Kabir Yusuf ya shawarci lauyoyi su rika faɗawa duk mutumin da ya kawo musu ƙara mara kyau gaskiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jhar Kano - Mai martaba sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya bayyana cewa babu kasar da za ta ci gaba matuƙar ana take gaskiya da adalci a shari'a.

Basaraken da aka mayar kan sarauta kwanan nan ya faɗi haka ne a lokacin da yake jawabi a wurin buɗe taron kungiyar lauyoyi ta Najeriya (NBA) jiya Talata.

Kara karanta wannan

Rigimar sarautar Kano: Sanusi II ya samu goyon bayan kungiyar lauyoyin Najeriya

Muhammadu Sanusi II.
Sarki Muhammadu Sanusi ya ce babu ƙaaar da ta cu gaba ba tare da adalci ba Hoto: Sanusi Lamido Sanusi
Asali: Twitter

Jawabin Muhammadu Sanusi II a taron NBA

Kalaman Sarki Sanusi II na zuwa ne a daidai lokacin da rigimar sarautar Kano tsakaninsa da sarki na 15, Aminu Ado Bayero ta koma gaban kotu, Leadership ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wasu na ganin gayyatar da ƙungiyar lauyoyi NBA ta yiwa Sanusi II da kuma ba shi damar jawabi a wurin taron wata alama ce da ke nuna ta amince shi ne sahihin sarki

Taron ya gudana a ɗakin taro na Amani da ke birnin Kano kuma ya samu halartar shugaban kotunan ɗa'ar ma'aikata, Mai shari'a Benedict Bakwaph Kanyip da shugaban NBA, Yakubu Maikyau (SAN).

Shugabar alkalan Kano, Mai Shari'a Dije Aboki da wasu manya-manya a ɓangaren shari'a sun halarci taron, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Sarki Sanusi II ya ja hankali kan adalci

Kara karanta wannan

Sarautar Kano: Abin da Sarki Sanusi II ya gargadi hakimai da ciyamomi 44 a kai a fadarsa

Da yake jawabi a wurin, Sarki Sanusi II wanda ya samu wakilcin Walin Kano, Mahe Bashir Wali, ya yi wa mahalarta taron maraba.

Sarkin ya kuma ya shaida musu cewa Kano tana da daɗaɗɗen tarihi a matsayin cibiyar al'adu da kasuwanci ta yankin Arewa.

Ya ce taken taron, "Adalci a Najeriya: ƙalubale da gyara," na nuni da cewa adalci shi ne ƙashin bayan al'umma domin sai da adalci ake samun zaman lafiya da ci gaba.

Gwamnan Kano, Abba ya shawarci lauyoyi

A nasa jawabin, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ƙalubalanci lauyoyi bisa umarnin kotu masu cin karo da juna a rikicin sarautar Kano.

Abba, wanda ya samu wakilcin sakataren gwamnatinsa, Abdullahi Baffa Bichi, ya buƙaci lauyoyin su riƙa gayawa mutane gaskiya idan suka kawo masu kara mara kyau.

Ya ce duk da gaskiya ɗaci gare ta, amma zai fi kyau a gaya wa nutum gaskiya maimakon lauya ya karɓi shari'ar da ya san ta take doka.

Kara karanta wannan

Babu alamun warware rikicin sarautar Kano bayan ganawar Gwamna Abba da NSA

Kano: Abba ya samu mafita daga ƙungiya

A wani rahoton kuma wata ƙungiya ta fito ta ba gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf shawara yayin da ake cikin rigimar masarautar Kano.

Ƙungiyar ta buƙaci gwamnan ya mayar da hankali wajen sauke nauyin al'ummar jihar Kano da ke wuyansa ba ya tsaya yana ce-ce-ku-cen siyasa ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel