NOA: Gwamnatin Tarayya Ta Fitar da Sanarwa Game da Sabon Taken Najeriya

NOA: Gwamnatin Tarayya Ta Fitar da Sanarwa Game da Sabon Taken Najeriya

  • Hukumar wayar da kan 'yan kasa (NOA) ta fitar da sabuwar sanarwa a yau Talata game da sabon taken Najeriya
  • Mataimakin daraktan yada labarai na hukumar, Paul Odenyi ne ya fitar da sanarwar ga manema labarai a Abuja
  • Sanarwar ta ƙunshi gyare-gyare da sauransu da hukumar za ta yi a kan sabon taken da Bola Tinubu ya kawo

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Nigeria - Hukuma mai wayar da kan 'yan kasa (NOA) ta fitar da sabuwar sanarwa kan gyare-gyaren da ta ke a kan taken Najeriya.

Hukumar ta ce a halin yanzu tana tattaunawa ne da masu ruwa da tsaki kan sauye-sauyen da za a yiwa sabon taken.

Kara karanta wannan

Kasar Saudiyya ta dauki tsauraran matakai kan masu zuwa hajji ta barauniyar hanya

Shugaba Tinubu
Hukumar NOA na kokarin tace sabon taken Najeriya. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta ruwaito cewa mataimakin daraktan yada labarai na hukumar ne ya sanar da haka a yau Talata a Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Za a yi gyara ga taken Najeriya

Hukumar ta ce bayan canza taken an samu wanda suka rika yada wanda ba a tace ba a kafafen sadarwa.

Saboda haka ta sanar da cewa za ta fitar taken da aka tace nan ba da jimawa ba domin kaucewa amfani da wanda bai dace ba.

Jama'a sun koka da taken Najeriya

Hukumar NOA ta ce ta samu bayanai kan cewa 'yan Najeriya na ta kokarin haddace sabon taken, rahoton TVC

Sai dai duk da kokarin, sun koka kan rashin samun cikakken bayani da kuma samun taken da aka tace.

Matakin da NOA ta dauka

Bayan tattara korafin da jama'a suka shigar hukumar NOA ta ce a yanzu haka tana tattaunawa kan gyare-gyaren da za ayi domin wayar da kan al'umma.

Kara karanta wannan

InnaliLahi: Mutane 30 sun mutu a wani mummunan ibtila'i da ya rutsa a Arewa

Ta kuma yi kira ga jami'an gwamnati idan za su yi amfani da taken su tuntubi jami'an NOA domin samun asalin taken a wajensu.

Za a kashe N20bn kan titi a Gombe

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin jihar Gombe za ta gina titi mai tsawon kilomita 18 kan kudi Naira biliyan 20 a fadin jihar.

Gwamnatin ta ayyana titin asibitin koyarwa na gwamnatin tarayya zuwa kolejin ilimi da fasaha da ke cikin garin cikin inda aikin zai shafa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng