Bayan Sace Mutum 150, Ƴan Bindiga Sun Ƙara Yin Garkuwa da Mutane Sama da 50 a Arewa
- Ƴan bindiga sun yi garkuwa da mutane 56 a kauyuka biyu da ke yankin kananan hukumomin Munya da Tunga a jihar Neja
- Shugaban ƙaramar hukumar Munya, Alhaji Aminu Najume ya tabbatar da sace mutanen, inda ya ce maharan sun nemi kuɗin fansa
- Wannan na zuwa ne kusan mako guda bayan ƴan bindiga sun ɗauke mutum 150 a kauyen Kuchi, sun nemi fansar N150m
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Niger - Ƴan bindiga sun yi awon gaba da mutum 30 a ƙauyen Kakuru da ke ƙaramar hukumar Munya a jihar Neja.
Har ila yau a wani harin na daban, ƴan bindiga sun sace mutane 26 daga ƙauyen Adogo Mallam, shi kuma a ƙaramar hukumar Tunga duk a jihar Neja.
Maharan sun aikata wannan ta'adi na garkuwa da mutane a ƙauyukan tsakanin ranar Lahadi zuwa Litinin, kamar yadda The Nation ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Yan bindiga sun nemi kuɗin fansa
Shugaban karamar hukumar Munya, Alhaji Aminu Najume, ya tabbatar da sace karin mutane 30 a kauyen Kakuru, inda ya ce maharan sun nemi kuɗin fansa.
"Mutum biyu ne kawai suka sako da nufin su lalubo kudi su biya a sako ‘yan uwansu. Sun sako wani mutum da aka yi garkuwa da shi tare da matarsa da ‘ya’yansa uku don ya je ya tattaro kudin fansa."
Shugaban ƙaramar hukumar ya koka kan rashin tura jami'an tsaro yankin, wanda a yanzu mutane sun tashi daga gidajen su saboda rashin tsaro.
Hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Neja ta kuma tabbatar da sace mutane 26 a yankin karamar hukumar Shiroro.
Miyagun 'yan bindiga sun sace mutane 150
Ƙauyen Kakuru da aka sace mutane 30 na da tazarar kilomita biyar daga garin Kuchi inda ƴan bindiga suka sace mutane 150 a makon jiya.
‘Yan ta’addan da suka sace mutane 150 a Kuchi sun nemi a biya fansa N150m, watau N1m kan kowane mutum ɗaya, sun sanya wa'adin 15 ga watan Yuni.
Sun ce idan ba a biya kuɗin ba, za su riƙa kashe mutum biyar a kowace rana har zuwa lokacin da za su biya kuɗin fansar, Premium Times ta ruwaito wannan.
'Yan bindiga sun kashe kansila
A wani rahoton, an ji kuma miyagun ƴan bindiga sun kashe kansila da shugaban matasa a kauyen Isu da ke ƙaramar hukumar Onicha a jihar Ebonyi.
Majiyoyi sun bayyana cewa maharan sun tare mutanen biyu, suka bude masu wuta sai da suka tabbatar sun mutu, sannan suka gudu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng