Miyagun 'Yan Bindiga Sun Kashe Ɗan Majalisar Yanki da Shugaban Matasa

Miyagun 'Yan Bindiga Sun Kashe Ɗan Majalisar Yanki da Shugaban Matasa

  • Miyagun ƴan bindiga sun kashe kansila da shugaban matasa a kauyen Isu da ke ƙaramar hukumar Onicha a jihar Ebonyi
  • Majiyoyi sun bayyana cewa maharan sun tare mutanen biyu, suka bude masu wuta sai da suka tabbatar sun mutu, sannan suka gudu
  • Kauyen Isu na fama da hare-hare da kashe-kashen rayuka a baya-bayan nan, ya haɗa iyaka da Enugu da kauyen Agba a Kudu maso gabas

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Ebonyi - Wasu ƴan bindiga sun hallaka mutum biyu, Stanley Akpa Nweze da Arinze Joshua Ugochukwu a kauyen Isu da ke ƙaramar hukumar Onicha a Ebonyi.

Ɗaya daga cikin waɗanda maharan suka kashe, Mista Nweze shi ne kansila mai wakiltar gundumar Enuagu a majalisar ƙaramar hukumar Onicha.

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: An kama wani hatsabibin ɗan bindiga a Zariya, ya fara tona asirin wasu

Yan sandan Najeriya.
Yan bindiga sun harbe kansila da shugaban matasa har lahira a jihar Ebonyi Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Twitter

'Yan bindiga sun kashe jagoran matasa

Ɗayan mutumin da aka kashe a harin, Arinze Joshua Ugochukwu, ya kasance shugaban ƙungiyar matasan Najeriya (NYCN) reshen Onicha a jihar Ebonyi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

The Nation ta rahoto cewa ‘yan bindigar sun kai wa Stanley da Arinze hari tare da kashe su a ranar Litinin a yankin Amanator da ke ƙauyen Isu.

Yadda aka kashe kansila a Ebonyi

Wasu majiyoyi daga yankin sun shaida cewa matasan biyu na kan babur suna tafiya zasu dawo Isu lokacin da ƴan bindigar suka tare su.

Maharan sun buɗe masu wuta nan take, sai da suka tabbatar duk sun mutu sannan suka bar wurin, in ji majiyoyi.

Haka nan kuma ƴan bindigar sun ci gaba da harbi a iska domin tsorata masu wucewa kafin daga bisani suka tsere zuwa cikin daji, Premium Times ta ruwaito.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda sun salwantar da ran basarake a Taraba watanni 5 da kashe kaninsa

Wane mataki hukumomi suka ɗauka?

Shugaban karamar hukumar Onicha, Chidiebere Uzor Agwu, yayin da yake tabbatar da faruwar lamarin, ya bayyana kaduwarsa da kashe matasan biyu kwatsam. 

A cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Prince Chijioke Agwu, mai magana da yawun ciyaman, Agwu ya bayyana lamarin a matsayin wani abin takaici. 

Ya kuma yi kira ga jami’an tsaro da su yi duk abin da za su iya domin ganin an kama masu laifin tare da hukunta su, zuwa yanzu ba a ji komai ba tukuna.

DCP Abubakar ya rasu a Ofis

A wani rahoton kuma, an ji rundunar ƴan sandan Najeriya ta shiga jimami yayin da babban jami'inta ya riga mu gidan gaskiya a ofishinsa a Abuja.

Mataimakin kwamishinan ƴan sanda, DSP Abubakar Muhammad Guri ya rasu jim kaɗan bayan ya shiga ofis a hedkwatar ƴan sanda.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262