Dubu Ta Cika: An Kama Wani Hatsabibin Ɗan Bindiga a Zariya, Ya Fara Tona Asirin Wasu

Dubu Ta Cika: An Kama Wani Hatsabibin Ɗan Bindiga a Zariya, Ya Fara Tona Asirin Wasu

  • Ƴan sanda sun kama wani tsoho ɗan shekara 70 a duniya wanda ake zargin ɗan bindiga ne a Zariya da ke jihar Kaduna
  • Rundunar ƴan sanda ta bayyana cewa dattijon ya fara ba da haɗin kai domin kama dukkan waɗanda ke taimaka masa
  • Bayan haka ƴan sanda sun cafke wasu masu garkuwa 3 da suka addabi al'umma a Saminaka, ƙaramar hukumar Lere a Kaduna

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Zaria, jihar Kaduna - Hukumar 'yan sanda a jihar Kaduna ta kama wani dattijo mai shekaru 70 da ake zargin dan bindiga ne a Zariya, ta cafke wasu mutum uku a Lere.

Dakarun ƴan sanda na caji ofis a Tudun Wada ne suka yi nasarar cafke wanda ake zargi mai suna, Hussaini, mazaunin Tudun Jukun a cikin Zariya.

Kara karanta wannan

Bayan sace mutum 150, ƴan bindiga sun ƙara yin garkuwa da mutane sama da 50 a Arewa

Sufetan yan sanda, IGP Kayode.
'Yan sanda sun kama ɗan bindiga dan shekara 70 da wasu mutane uku a Kaduna Hoto: PoliceNG
Asali: Facebook

Jami'an 'yan sanda sun cafko tsoho

Kamar yadda Channels tv ta ruwaito, Husaini ya shiga hannu ne bayan ƴan sanda sun samu sahihan bayanan sirri kan zirga-zurgarsa a yankin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mai magana da yawun hukumar ƴan sandan jihar Kaduna, Mansir Hassan ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar.

Ƴan sanda sun kwato makamai

Ya ce jami'an tsaron sun kwato bindiga kirar AK-47, bindigar gida, da harsashi guda uku a hannunsa.

"Bayan tattara bayanan sirri, DPO na Tudun Wada ya jagoranci dakarun ƴan sanda suka kama Hussaini, ɗan shekara 70 a duniya daga yankin Tudun-Jukun a Zariya.
"An kama mutumin da misalin karfe 02:50 na dare kuma a yayin samamen, an kwato bindiga kirar AK-47, bindigar gida, da harsashi guda uku daga hannun wanda ake zargin.
"Wanda ake zargin yana ba ƴan sanda haɗin kai wajen kama sauran abokan aikinasa kuma nan ba da jimawa ba za a gurfanar da shi a gaban kotu.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga da yawa sun mutu da jirgin sojoji ya yi ruwan bama-bamai a jihohi 2

Ƴan sanda sun kama masu garkuwa a Kaduna

Vanguard ta rahoto cewa wasu ƴan bindiga uku da suka addabi mutane da hare-haren garkuwa da mutane sun shiga hannu a ƙaramar hukumar Lere duk a Kaduna.

Kakakin ƴan sanda ya jero sunayen waɗanda aka kama, Isah Baffa Rabo daga kauyen Maibindiga, Ja’afaru Sale daga kauyen Durumi da Umar Musa daga kauyen Durumi duk a Lere.

Mutum 30 sun mutu a jihar Niger

A wani rahoton kuma ana fargabar ruftawar ramin haƙar ma'adanai ya zama ajalin aƙalla mutane 30 a jihar Neja ranar Litinin, 3 ga watan Yuni da daddare.

Rahotanni sun nuna cewa zuwa yanzun an zaro mutum shida da rai yayin da ake ci gaba da aikin ceto a wurin da ibtila'in ya faru a Shiroro.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel