InnaliLahi: Mutane 30 Sun Mutu a Wani Mummunan Ibtila'i da Ya Rutsa a Arewa
- Ana fargabar ruftawar ramin haƙar ma'adanai ya zama ajalin aƙalla mutane 30 a jihar Neja ranar Litinin, 3 ga watan Yuni da daddare
- Rahotanni sun nuna cewa zuwa yanzun an zaro mutum shida da rai yayin da ake ci gaba da aikin ceto a wurin da ibtila'in ya faru a Shiroro
- Hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar (NSEMA) ta tabbatar da faruwar lamarin amma gwamnatin Neja ba ta ce komai ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Niger - Rahotanni sun nuna cewa akalla mutane 30 ne ake fargabar sun mutu sakamakon ruftawar ramin hakar ma'adinai a jihar Neja.
Ramin ya rufta kan mutanen ne a kauyen Galkogo da ke karamar hukumar Shiroro a jihar da ke Arewa ta Tsakiya a Najeriya.
Jaridar Leadership ta tattaro cewa wannan ibtila'in ya auku ne jiya Litinin, 3 ga watan Yuni, 2024 da daddare kuma zuwa yanzu an ceto mutane shida ɗauke da raunuka.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mai magana da yawun hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Neja (NSEMA), Ibrahim Hussein, ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai.
NSEMA ta faɗi halin da ake ciki
A wata sanarwa da ya fitar, shugaban NSEMA ya ce aikin ceto waɗanda ramin ya faɗa kansu ya gamu da cikas saboda yanayin wurin da hare-haren ƴan bindiga.
"NSEMA ta samu rahoton rugujewar ramin hakar ma’adinai a kauyen Galkogo na karamar hukumar Shiroro. Wurin hakar mallakar wani kamfani ne mai suna African Minerals and Logistics Limited.
"Wurin ya rufta ne sakamakon ruwan sama mai ƙarfi wanda ya sa kasar wurin ta yi laushi," in ji sanarwar.
Shugaban hukumar bai bayyan adadin mutanen da ramin ya rufta kansu ba, kamar yadda The Cable ta ruwaito.
Wane mataki hukumomi suka ɗauka?
Amma har kawo yanzu da muke haɗa wannan rahoton, ma’aikatar ma’adanai ta jihar Neja ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance kan lamarin ba.
Wasiu Abiodun, mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Neja, bai amsa kiran waya ko sakonnin salula da aka tura masa kan lamarin ba.
Muhammad Sani, wani mazaunin yankin ya tabbatar da faruwar ibtla'in ga Legit Hausa, ya ce abun damuwar shi ne har yanzun ba a ciro mutanen da ƙasar ta danne ba.
Ya ce:
"A Galadima Kogo ne lamarin ya faru, ruwan sama aka yi mai yawa, to wurin an tara ƙasa mai yawa, kuma abun ya zo da tsautsayi da ƙarar kwana."
"Har yanzun ba a gama ciro waɗanda ƙasa ta rufta kansu ba, Allah ya jiƙansu domin da wahala a ƙara samun wani yana numfashi."
Fasto ya faɗi mafita ga ƴan Najeriya
A wani rahoton kuma babban limamin cocin RCCG, Fasto Enoch Adejare Adeboye, ya koka kan halin ƙunci da wahalar rayuwar da ƴan Najeriya suka tsinci kansu.
Ya ce halin da kasar nan ke ciki abin kyama ne kuma mutane da yawa ba za su iya jurewa ba yayin da yajin aikin NLC ya kankama.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng