'Yan Bindiga da Yawa Sun Mutu da Jirgin Sojoji Ya Yi Ruwan Bama Bamai a Jihohi 2

'Yan Bindiga da Yawa Sun Mutu da Jirgin Sojoji Ya Yi Ruwan Bama Bamai a Jihohi 2

  • Rundunar sojojin sama ta yi ruwan wuta kan sansanonin manyan ƴan bindiga a jihohin Kaduna da Katsina da ke Arewa maso Yamma
  • Yayin luguden wutar da sojojin suka yi, ƴan bindiga da dama sun bakunci lahira kuma an lalata kayan aiki da sansaninsu
  • Sojojin sun samu wannan nasara ne a ƙaramar hukumar Giwa a Kaduna da yankin karamar hukumar Ƙanƙara a jihar Katsina

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Luguden wutar da rundunar sojojin saman Najeriya ya yi kaca-kaca da sansanin ƴan bindiga a yankin ƙaramar hukumar Giwa a jihar Kaduna.

Mai magana da yawun rundunar sojin sama (NAF), Edward Gabkwet ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya rattabawa hannu ranar Talata.

Kara karanta wannan

Matawalle ya dauki zafi kan kisan sojoji a Abia, ya fadi matakin dauka

Jirgin NAF.
Sojojin sama sun murkushe ƴan bindiga da dama a jihohin Kaduna da Katsina Hoto: Nigeria Air Force
Asali: Facebook

Gabkwet ya ce dakarun rundunar sojin Operation Whirl sun kai wannan samame ta sama ne a tsakanin ranakun 30 da 31 ga watan Mayun 2024, Channels tv ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce:

"Sojojin sama sun saki ruwan bama-bamai a sansanin kasurgumin ɗan bindiga, Buharin Yadi da ke jejin Bula a ƙaramar hukumar Giwa ya jihar Kaduna.
"An kai wannan samamen ne bayan tattara bayanan sirrin wurin da ake hari, inda aka gano tarkace da bukkoki a cikin ƙungurmin jejin."

Sojoji sun kashe ƴan bindiga a Kaduna

Bayanan da aka tattara sun nuna an hangi ƴan bindiga ɗauke da mugayen makamai a wurin, kuma an hangi babura 13 a karaƙashin wata bishiya.

A cewar kakakin NAF, daga nan ne rundunar sojojin ta tura ɗaya daga cikin jiragen yaƙi ya kai farmaki wurin bayan gano ƴan bindigar na da hannu a hare-haren Birrnin Gwari da Giwa.

Kara karanta wannan

An rasa rayuka bayan 'yan bindiga sun farmaki kauyukan jihar Katsina

Ya ce a binciken da aka yi daga bisani ya nuna cewa ƴan bindiga da dama sun bakunci lahira yayin da farmakin ya ƙona sansaninsu a dajin.

An samu nasara kan 'yan bindiga a Katsina

Rundunar sojin sama ta Operation Hadarin Daji ta kai hare-hare makamancin wannan a ranar 2 ga watan Yunin 2024 a jihar Katsina, rahoton Leadership.

Sojojin sun saki bama-bamai bayan samun bayanan sirri da gano wurin da shugaban ‘yan bindiga, Alhaji Iliya tare da tawagarsa suke a tsaunin Zango a karamar hukumar Kankara.

Bayan haka aka tura jirgin yaƙi ya ragargaji ƴan bindigar tare da lalata muhimman kayan aikinsu.

An sace malaman jami'ar Dutsinma

A wani rahoton kuma wasu lakcarori biyu a Jami'ar Tarayya a Dutsinma sun gamu da iftila'i bayan ƴan bindiga sun yi awon gaba da su a jihar Katsina.

Lamarin ya faru ne da safiyar jiya Litinin 3 ga watan Yuni a karamar hukumar Dutsinma da ke jihar a Arewacin Najeriya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262