Gwamnati Ta Bayyana Yadda Yajin Aikin ’Yan NLC Zai Kara Jefa Al’umma a Wahala
- Gwamantin tarayya ta ƙara kira ga kungiyar kwadago kan duba yiwuwar janye yajin aiki da ta shiga ranar Litinin
- A cewar gwamnatin, yajin aikin zai shafi rayuwar talakawa musamman wadanda suke rayuwa hanu baka hanu ƙwarya
- A ranar Litinin, 3 ga watan Yuni kungiyar kwadago ta shiga yajin aiki saboda karin albashin ma'aikata a Najeriya
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Nigeria - Gwamnatin tarayya ta kara bayyana wa kungiyar kwadago hadarin da yake cikin yajin aikin da ta fara a ranar Litinin.
Ministar kwadago, Nkeiruka Onyejeocha ce ta bayyana haka ga kungiyar a yayin wata hira da ta yi da 'yan jarida.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa ministar ta ce bai kamata kungiyar kwadago ta shiga yajin aiki alhali ana teburin tattaunawa ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda yajin aikin NLC zai shafi talaka
Ministar kwadago, Nkeiruka Onyejeocha ta ce idan yajin aikin ya cigaba zai ruguza tattalin Najeriya kuma zai shafi talakawa sosai.
Nkeiruka ta ce akwai talakawan da kullum sai sun fita su nemo abin da za su ci amma yajin aikin ya tsayar musu da hanyar samun abinci.
NLC: 'Yajin aiki zai shafi ilimi' - Gwamnati
Har ila yau, ministar ta bayyana cewa yajin aikin barazana ne ga cigaban ilimi da karantarwa a Najeriya, rahoton Daily Post.
Ta ce dalibai da suke zuwa makaranta sun dawo gida, wasu da suke rubuta jarrabawa dole sun tsaya.
Sauran harkokin rayuwa sun tsaya
Ministar ta kara da cewa a yanzu haka harkokin rayuwa sun tsaya a Najeriya baki daya kuma hakan ya shafi al'umma da dama.
Ta ce asibitoci sun kulle ga tarin marasa lafiya, ga shi harkokin kasuwanci sun dakata wanda hakan barazana ne ga kasar baki daya.
Saboda haka ta yi kira ga 'yan kwadago su duba yanayin rayuwar al'ummar kasar su janye yajin aikin.
An yi kira ga NLC kan batun Hajji
A wani rahoton, kun ji cewa kungiyar masu jigilar mahajjata a Najeriya sun koka kan yadda yajin aikin yan kwadago ke kokarin jawo tsaiko ga tafiyar mahajjata.
Kungiyar ta ce idan yajin aikin ya cigaba zai shafi addini da tattalin mahajjata ta inda za su yi asarar sosai kasancewar sun biya makudan kudi domin tafiya ibada.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng