Yajin Aikin NLC Ya Hana Jigilar Alhazai Zuwa Ƙasa Mai Tsarki? NAHCON Ta Faɗi Gaskiya

Yajin Aikin NLC Ya Hana Jigilar Alhazai Zuwa Ƙasa Mai Tsarki? NAHCON Ta Faɗi Gaskiya

  • NAHCON ta kwantar da hankalin maniyyata yayin da suka fara fargabar rasa damar sauke farali saboda yajin aikin ƴan kwadago
  • Hukumar ta bayyana cewa yajin aikin NLC ba zai dakatar da jigilar alhazai ba kuma idan Allah ya so za a kama kwashe su kafin 10 ga watan Yuni
  • Fatima Sanda Usara, mataimakiyar kakakin NAHCON ta ce a halim yanzu jirage uku zuwa shida ke tashi a kowace rana

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Hukumar jin daɗin alhazai ta ƙasa (NAHCON) ta ce yajin aikin da kungiyar kwadago (NLC) ta shiga ba zai shafi jigilar maniyyata zuwa ƙasa mai tsarki ba.

Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da mataimakiyar kakakin NAHCON ta ƙasa, Fatima Sanda Usara ta fitar bayan ƴan kwadago sun shiga yajin aiki ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Kungiyar ƙwadago ta janye yajin aiki, ta ba gwamnatin tarayya wa'adin mako 1

Jigilar alhazan Najeriya.
Yajin aiki ba zai hana jigilar maniyyata ba a Najeriya in ji NAHCON Hoto: National Hajj Commission of Nigeria
Asali: Facebook

Yajin-aiki ba zai hana zuwa Hajji ba

Ta fahimci halin fargaba da maniyyatan suka shiga saboda yajin aikin, inda ta yi alƙawarin cewa za a kammala jigilar alhazai gaba ɗaya kafin 10 ga watan Yuni.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, sanarwar ta bayyana cewa sama da alhazai 37,102 ne aka kwashe zuwa Saudiyya a halin yanzu.

NAHCON ta faɗi yadda aiki ke tafiya

Sanarwar ta ce:

"Jiragen da ke jigilar maniyyata na ci gaba da aikinsu kamar yadda aka tsara tun farko, an fara da sawu uku kowace rana, amma yanzu ya ƙaru zuwa sawu shida a rana.
"A halin yanzun, hukumar NAHCON na tabbatar da an yi akalla sawu uku zuwa shida a kowace rana ya danganta da yadda aka tsara."

Maniyata nawa suka rage a Najeriya?

Ta ƙara da cewa akwai kimanin maniyyata 13,176 har yanzun ba a kwashe su ba kuma wannan adadin zai ragu kafin ƙarewar jiya Litinin saboda wasu jiragen za su tashi.

Kara karanta wannan

Gwamnati ta bayyana yadda yajin aikin 'yan NLC zai kara jefa al'umma a wahala

"Ragowar adadin maniyyatan da har yanzu suke nan gida ya nuna cewa saura sawu ɗaya a jihohin Kaduna, Gombe, Borno, Zamfara, Adamawa, Kebbi da Abuja mai ragowar alhazai 33."
"Jirgi ɗaya zai kwashe dukkan alhazan Kudu maso Kudu kuma za a samu ragowar kujeru. Ba a fara jigilar maniyyatan Taraba mai mutum 100 ba. Aiki ya yi nisa a Jigawa, Kwara, Neja da Sakkwato."

- Fatima Usara.

AHOUN ta roƙi NLC ta janye yajin aiki

A wani rahoton kuma kungiyar masu jigilar mahajjata ta kasa (AHOUN) ta yi kira na musamman ga kungiyar kwadago kan yajin aiki da ta shiga.

Cikin sakon ta kungiyar ta wallafa ta nuna cewa duk da muhimmancin yajin aikin ga rayuwar ma'aikata, ya zo a lokacin da bai dace ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel