Yajin Aiki: Abubuwan da Aka Amince da Su a Taron Gwamnatin Tinubu da Ƴan Kwadago

Yajin Aiki: Abubuwan da Aka Amince da Su a Taron Gwamnatin Tinubu da Ƴan Kwadago

  • Wakilan gwamnatin tarayya da ƴan kwadago sun fito daga taron gaggawa da aka shirya kan mafi ƙarancin albashin ma'aikata a Najeriya
  • NLC da TUC sun tsunduma yajin aiki bayan gaza cimma matsaya da gwamnatin tarayya a taron da aka yi ranar 31 ga watan Mayu
  • Sa'o'i kaɗan bayan fara yajin aiki, sakataren gwamnati ya haɗa taro a ofishinsa da nufin tattauna yadda za a kawo karshen yajin aikin NLC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Rahotanni sun bayyana cewa an ƙarkare taron gaggawa da gwamnatin tarayya ta kira ƴan kwadago kan yajin aikin da aka fara yau.

Idan baku manta ba muna kawo rahoton cewa shugabannin ƴan kwadago sun isa ofishin sakataren gwamnatin tarayya domin shiga taron gaggawa da aka gayyace su.

Kara karanta wannan

Yajin aiki: Sojoji sun kewaye wurin taron ƴan kwadago da ƙusoshin gwamnati a Abuja

Bola Tinubu da NLC.
An gama taron gaggawa tsakanin gwamnatin tarayya da yan kwadago Hoto: @aonanuga1956
Asali: Twitter

TABLE OF CONTENTS

TVC News ta kawo cewa a halin yanzun gwamnati da ƴan kwadago sun ƙarkare taron na yau Litinin 3 ga watan Yuni, 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wace matsaya aka cimma a zaman?

Gwamnatin tarayya karkashin Bola Ahmed Tinubu ta amince za ta kara wani abu a tayin N60,000 da ta yi a matsayin mafi ƙarancin albashi.

A rahoton Daily Trust, sanarwar da aka fitar bayan kammala taron ta nuna cewa:

“Shugaban kasa kuma babban Kwamandan askarawan Najeriya, ya shirya tsaf domin biyan mafi karancin albashin ma’aikata wanda ya haura N60,000;
"Sakamakon haka kwamitin da aka kafa mai ɓangarori uku kan mafi karancin albashi zai ci gaɓa da zama a kowace rana a mako na gaba domin cimma matsaya.
"Saboda haka duba da girman shugaban kasa, ƴan kwadago za su koma gida su yi shawara da sauran rassansu domin yin nazari kan wannnan alƙawari.

Kara karanta wannan

Yajin aiki: Ƴan ƙwadago sun dira ofishin SGF a Abuja, za a sa labule da jiga-jigan gwamnati

Tasirin yajin aikin 'yan kwadago

A kwana daya da suka suna yajin aiki ƴan kwadago sun kulle makarantu, bankuna, ofisoshin gwamna da sauran muhimman wurare.

A dalilin yajin aikin an dauke wuta a kusan fadin Najeriya tun tsakar daren Lahadi.

Ma'aikata sun bi umarnin NLC a Kano

A wani rahoton kuma ma'aikatan gwamnati a Kano sun yi zamansu a gida yayin da NLC ta ayyana shiga yajin aiki daga yau Litinin, 3 ga watan Yuni

An kulle sakateriyar Audu Baƙo yayin da aka tsayar da duk wasu harkokin sufuri a filin sauka da tashin jiragen sama na Aminu Kano ban da jirgin alhazai.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262