Yajin aiki: Sojoji Sun Kewaye Wurin Taron Ƴan Kwadago da Kusoshin Gwamnati a Abuja

Yajin aiki: Sojoji Sun Kewaye Wurin Taron Ƴan Kwadago da Kusoshin Gwamnati a Abuja

  • NLC ta ankarar da cewa dakarun sojojin Najeriya sun kewaye wurin taron ƴan kwadago da wakilan gwamnatin tarayya
  • Shugabannin kwadagon sun isa ofishin sakataren gwamnatin tarayya bayan an gayyace su zuwa taron gaggawa ranar Litinin
  • NLC da TUC sun ayyana shiga yajin aiki ne bayan gwamnati ta gaza biyan buƙatarsu kan batun mafi ƙarancin albashi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Shugabannin ƴan kwadago sun koka kan yadda suka ga dakarun sojoji sun kewaye wurin da aka shirya taronsu da wakilan gwamnatin tarayya.

Hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa da ƙungiyar NLC ta wallafa a shafinta na manhajar X ranar Litinin, 3 ga watan Yuni, 2024.

Kara karanta wannan

Yajin aiki: Abubuwan da aka Amince da su a taron Gwamnatin Tinubu da ƴan ƙwadago

Yan kwadago da Tinubu.
NLC na zargin sojoji sun kewaye wurin tattaunawar su da wakilan gwamnatin tarayya Hoto: @NLCHeadquaters, @OfficialABAT
Asali: Twitter

Ƴan kwadagon sun ankarar da halin da suke ciki ne jim kaɗan bayan sun isa ofishin sakataren gwamnatin tarayya (SGF).

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

NLC ta ɗauki zafi kan zuwa sojoji

Kungiyar kwadagon ta yi barazanar cewa idan gwamnati ta yi wani yunkurin tursasa shugabanninta, ta kwana da shirin kara dagula lamarin.

Ɗaya daga cikin saƙonnin da NLC ta wallafa shafinta ya ce:

"Yanzu haka dakarun sojoji sun kewaye wurin da aka shirya taron ƴan kwadago da wakilan gwamnatin tarayya a harabar ofishin SGF.
"Saboda haka ba za mu yarda da duk wani yunkuri na tsoratar da shugabannin mu ko a tursasa su ba, hakan zai kara dagula lamarin, zamu tafi yajin da babu ranar janye shi.
"Shugabanninmu suna aiki ne a kan matsayar da muka amince da ita, ba gaban kan su suke yi ba, nasara ƙungiyar kwadago, nasara ma'aikatan Najeriya.

Kara karanta wannan

Yajin aiki: Ƴan ƙwadago sun dira ofishin SGF a Abuja, za a sa labule da jiga-jigan gwamnati

Meyasa NLC ta shiga yajin aiki?

Ranar Jumu'a, 31 ga watan Mayu, kungiyar kwadago ta sanar da cewa za ta fara yajin aiki kan gazawar gwamnati wajen ƙara mafi ƙarancin albashi.

Shugaban NLC na ƙasa, Joe Ajaero, ya ce yajin aikin zai fara ne da tsakar daren ranar Lahadi, 2 ga watan Yuni, 2024.

Gwamnati ta kira zama bayan shiga yajin aiki

A wani rahoton kuma Gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagoranci Bola Ahmed Tinubu ta kira taron kwamitin da aka kafa kan sabon mafi karancin albashi.

NLC da TUC sun fice daga taron kwamitin wanda aka yi ranar 31 ga watan Mayu bayan gwamnati ta kafe kan N60,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262