Yajin Aiki: Ma'aikatan Gwamnati a Jihar Kano Sun Bi Umarnin Kungiyoyin NLC da TUC
- Ma'aikatan gwamnati a Kano sun yi zamansu a gida yayin da NLC ta ayyana shiga yajin aiki daga yau Litinin, 3 ga watan Yuni
- An kulle sakateriyar Audu Baƙo yayin da aka tsayar da duk wasu harkokin sufuri a filin sauka da tashin jiragen sama na Aminu Bando ban da jirgin alhazai
- Sai dai ƴan kwasuwa a manyan kasuwannin Kano sun fita sun ci gaba da harkokin su yayin da bankuna kuma duk an garƙame su
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kano - Ma'aikatan gwamnati a jihar Kano sun bi sahun takwarorinsu, sun tsunduma yajin aikin sai baba ta gani yau Litinin, 3 ga watan Yuni, 2024.
Wannan na zuwa ne bayan manyan kungiyoyin kwadago na ƙasa NLC da TUC sun sanar da shiga yajin aiki kan mafi ƙarancin albashin ma'aikata a Najeriya.
An rufe sakatariya a Kano saboda yajin-aiki
Wakilin jaridar Leadership ya tattaro cewa sakatariyar gwamnatin tarayya da ta jiha da ke Audo Bako an kulle su da kwaɗuna, babu ma'aikacin da ya fito aiki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wuraren aiki da aka saba gani cike da jama'a har da cunkoso sun zama babu kowa yau Litinin saboda ma'aikata ba su fito aiki ba.
Ƴan kasuwa sun fita aiki a Kano
Amma a ɓangaren ƴan kasuwa kuwa, babu abin da ya sauya, mutane sun ci gaba da harkokin su na kasuwanci a jihar Kano.
Kasuwar IBB, kasuwar Kantin Kwari, Kasuwar Rimi da kasuwar hada-hadar wayoyi Farm Centre ba ma su san ana yajin aiki ba, mutane suna harkokin su na yau da kullum.
Ayyuka sun tsaya a filin Aminu Kano
A filin jirgin sama na Aminu Kano kuma, jiragen da ke jigilar alhazai ne kawai aka bari suka tashi amma duk wani jirgin sama an dakatar da shi saboda yajin NLC.
Bugu da ƙari, dukkan bankuna a kwaryar birnin Kano a kulle suke ba su aiki, kamar yadda Daily Post ta rahoto.
Ƴan kwadago sun bayyana cewa wannan yajin aikin babu wasa a cikinsa saboda sun fahimci gwamnatin tarayya ba ta ɗauki batun mafi ƙarancin albashi da gaske ba.
An rufe makarantu a Kano
Wani malamin makaranta a Kano, Malam Sanusi, ya tabbatarwa Legit Hausa cewa an rufe makarantu saboda yajin aikin da aka fara.
A cewarsa, wasu iyayen sun kira su a waya domin tabbatar da za a yi makaranya ko kuwa sun shiga yajin aiki, wasu kuma sai da suka je suka gani da idonsu.
"Babu wanda ya fita aiki jiya Litinin, na san dai a makarantar mu an samu iyayen da suka je domin tabbatarwa, wasu kuma a waya suka kira mu."
Gwamnati ta kira taro da NLC
A wani rahoton kuma kun ji cewa yayin da yajin aiki ƴan kwadago ke ƙara kankama, gwamnatin tarayya ta kira taron kwamitin mafi ƙarancin albashi.
Hukumar kula da albashi da kuɗin shiga ta ƙasa (NSIWC) ce ta kira taron wanda zai gudana ranar Talata, 4 ga watan Yuni, 2024.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng