Yajin Aikin NLC Ya Taɓa Sufurin Jirgin Ƙasan Kaduna Zuwa Abuja

Yajin Aikin NLC Ya Taɓa Sufurin Jirgin Ƙasan Kaduna Zuwa Abuja

  • Jirgin ƙasan da ke zirga-zirga tsakanin Kaduna zuwa Abuja ya bi sahun ƙungiyoyin kwadago wajen shiga yajin aiki yau Litinin
  • Shugaban AKTS, Yusuf Kazeem ya bayyana cewa ma'aikatan sufurin jiragen kasa ba su fito aiki ba kuma babu jirgin da ya shigo ko ya fita daga Abuja
  • Wannan na zuwa ne yayin da ƙungiyoyin kwaɗago na ƙasa suka fara yajin aiki kan mafi ƙarancin albashin ma'aikata a Najeriya

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Zirga-zirgar jiragen ƙasa daga Kaduna zuwa Abuja ta tsaya cik a yau Litinin, 3 ga watan Yuni, 2024 sakamakon yajin aikin da ƴan kwadago suka fara.

Rahotanni sun nuna babu wani jirgin ƙasa da ya tashi daga tashar Rigasa Kaduna zuwa Abuja ko kuma ya taso daga tsashar Idu a Abuja zuwa Kaduna a yau Litinin.

Kara karanta wannan

Sanusi II Vs Aminu: NLC ta kawo babban cikas a a kotu kan rigimar sarautar Kano

Jirgin ƙasa.
Jirgin kasar Kaduna zuwa Abuka ya bi sahun NLC Hoto: Willy Ibimina
Asali: Twitter

Shugaban ƙungiyar sufurin jirgin Kaduna-Abuja (AKTS), Kwamared Yusuf Kazeem ya ce babu jirgin ƙasan da ya shigo ko ya fita daga Abuja a yau.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ma'aikata sun bi umarnin NLC

A rahoton The Nation, Kazeem ya ce:

"An yi biyayya ga umarnin shiga yajin aikin saboda babu zirga-zirgar jiragen ƙasa kwata-kwata yau. Babu fasinjoji da suka zo saboda mun tura masu saƙon tes cewa jirgi ba zai yi aiki ba .
"Daman ta intanet muke sayar da tikiti kuma bamu buɗe shafin sayen tikitin ba wanda ya nuna alamar cewa babu aiki.
"Wasu fasinjojin sun kira waya suna ƙorafin cewa sun gaza sayen tikitin, hakan ya sa muka yi amfani da wannan dama wajen sanar musu cewa za mu tafi yajin aiki."

Yadda yajin aikin NLC ya kankama

Ya ƙara da cewa ma'aikatan tsahar jirgin ba su fito aiki ba ranar Litinin saboda shiga yajin aikin.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta gargadi ma'aikata ana dab da fara yajin aiki

“Ma’aikatan mu ma ba su fito aiki ba saboda suna da masaniyar fara yajin aikin," in ji shi.

Ƙungiyar kwadago NLC da takwararta TUC sun ayyana shiga yajin aiki ne saboda gazawar gwamnati wajen cika masu bukatarsu kan mafi ƙarancin albashi, cewar rahoton Pulse.

NLC ta hana zaman kotu a Kano

A wani rahoton kun ji cewa Babbar kotun tarayya ta ɗage sauraron ƙarar da aka shigar gabanta kan dambarwar masarautar Kano tsakanin Sanusi II da Aminu Ado.

Hakan ta faru ne sakamakon yajin aikin da ƴan kwadago suka fara wanda ya hana zaman kotun ranar Litinin, 3 ga watan Yuni, 2024.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262