ASUU Ta Bayyana Matsayarta Kan Shiga Yajin Aikin Kungiyoyin Kwadago

ASUU Ta Bayyana Matsayarta Kan Shiga Yajin Aikin Kungiyoyin Kwadago

  • Ƙungiyar malaman jami'o'i ta Najeriya (ASUU) ta shiga cikin yajin aikin da ƙungiyoyin ƙwadago na NLC da TUC suka fara a faɗin ƙasar nan
  • ASUU ta umarci mambobinta da ke jami'o'in da su shiga yajin aikin da aka fara a ranar Litinin, 4 ga watan Yuni bayan an kasa cimma matsaya tsakanin ƴan ƙwadago da gwamnatin tarayya
  • Ƙungiyoyin ƙwadagon dai sun buƙaci gwamnatin tarayya da ta biya N494,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi yayin da gwamnatin ta kafe a N60,000

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Ƙungiyar malaman jami’o’i ta Najeriya (ASUU) ta umurci ɗaukacin mambobinta na ƙasa baki ɗaya da su shiga yajin aikin da ƙungiyoyin ƙwadago suka fara.

ASUU ta umarci mambobinta da su shiga yajin aikin tare da sauran ma'aikatan Najeriya a ranar Litinin, 3 ga watan Yunin 2024.

Kara karanta wannan

'Yan Najeriya sun taso hadimin Tinubu a gaba kan batun yajin aikin NLC, TUC

ASUU ta shiga yajin aiki
ASUU ta umarci mambobinta su shiga yajin aikin NLC da TUC Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Yajin aiki: Wane umarni ASUU ta ba da?

Ƙungiyar ta kuma umurci shugabannin rassanta na jami’o’i daban-daban da su haɗa kan ƴan ƙungiyar da ke ƙarƙashinsu domin bin umarnin shiga yajin aikin, cewar rahoton jaridar Tribune.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƙungiyar ASUU ta bayar da wannan umarni ne a wata takarda mai ɗauke da kwanan watan 2 ga watan Yunin 2024, mai ɗauke da sa hannun shugabanta na ƙasa Farfesa Emmanuel Osodeke.

Takardar an aika da ita ga dukkan shugabannin rassan ƙungiyar na jami'o'i da jagororin ƙungiyar na shiyya-shiyya, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar.

"NLC ta sanar da fara yajin aiki daga ranar Litinin, 3 ga watan Yunin 2024 sakamakon gazawar gwamnati wajen kammala tattaunawa kan mafi ƙarancin albashi da janye cire tallafin wutar lantarki."
"Ana umartar rassanmu da su shiga yajin aikin a matsayinmu na ƙungiyar da ke da alaƙa da ƙungiyar ƙwadago."

Kara karanta wannan

Yajin aiki ya jawo kungiyoyin kwadago sun kulle majalisar tarayya a Abuja

- Farfesa Emmanuel Osodeke.

Ƴan ƙwadago sun rufe majalisar tarayya

A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan ƙungiyar ma'aikatan majalisar tarayya (PASAN) sun kulle harabar majalisar tarayya da ke birnin Abuja.

Mambobin sun rufe kofofi biyu na shiga majalisar domin bin umarnin ƙungiyoyin ƙwadago na shiga yajin aikin sai baba ta gani a faɗin Najeriya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel