Sanusi II Vs Aminu: NLC Ta Kawo Babban Cikas a Kotu Kan Rigimar Sarautar Kano

Sanusi II Vs Aminu: NLC Ta Kawo Babban Cikas a Kotu Kan Rigimar Sarautar Kano

  • Babbar kotun tarayya ta ɗage sauraron ƙarar da aka shigar gabanta kan dambarwar masarautar Kano tsakanin Muhammadu Sanusi II da Aminu Ado Bayero
  • Hakan ta faru ne sakamakon yajin aikin da ƴan kwadago suka fara wanda ya hana zaman kotun ranar Litinin, 3 ga watan Yuni
  • Manyan kungiyoyin kwadago sun fara yajin aiki ne bayan gaza cimma matsaya da gwamnatin tarayya kan mafi ƙarancin albashi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kano - Yajin aikin da ma'aikata suka fara yau Litinin, 3 ga watan Yuni, 2204 ya kawo tsaiko a ci gaba da sauraron shari'a kan rikicin masarautar Kano.

Manyan ƙungiyoyin kwadago na ƙasa NLC da TUC sun shiga yajin aikin sai baba-ta-gani biyo bayan gaza cimma matsaya kan mafi ƙarancin albashi da ƙarin kuɗin wuta.

Kara karanta wannan

Yajin aiki: Ƴan ƙwadago sun dira ofishin SGF a Abuja, za a sa labule da jiga-jigan gwamnati

Sarki Sanusi da Aminu Ado Bayero.
NLC ta hana zaman sauraron ƙara kan rikicin masarautar Kano Hoto: Masarautar Kano
Asali: UGC

Sai dai a ranar farko da aka fara wannan yajin aiki ne babbar kotun tarayya mai zama a jihar Kano ta tsara fara sauraron shari'a kan rikicin masarautar Kano.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yajin aikin NLC ya hana zaman kotu

Wakilin Aminiya Hausa ya tattaro cewa alkalin da zai jagoranci shari'ar, mai shari'a Abdullahi Muhammad Liman ya halarci zaman kotun yau Litinin

Amma duk da alƙalin ya fita aiki kotun ta sanar da ɗage zaman sauraron ƙarar saboda yajin aikin da ma'aikata suka fara kuma ba ta faɗi ranar da za a dawo ba.

An shigar da ƙarar gaban kotun ne kan dambarwar kujerar sarauta tsakanin Muhammadu Sanusi II da Alhaji Aminu Ado Bayero.

Yadda aka fara rikicin sarautar Kano

Rikicin ya fara ne bayan majalisar dokokin jihar Kano ta rushe masarautu biyar da tsohon gwamna, Abdullahi Umar Ganduje ya ƙirƙiro a zamanin mulkinsa.

Kara karanta wannan

Yajin Aiki: Ma'aikatan gwamnati a jihar Kano sun bi umarnin kungiyoyin NLC da TUC

Jim kaɗan bayan haka Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sanar da mayar da Muhammadu Sanusi II kan karagar sarkin Kano bayan rattaba hannu kan dokar masarauta, 2024.

Hakan bai yiwa tsagin sarkin Ƙano na 15 daɗi ba, wanda ta kai ga suka shigar da ƙara kuma babbar kotun tarayya ta bayar da umarnin hana naɗin Sanusi II.

Kwatsam sai kuma aka ji babbar kotun jiha ta umarci Aminu Ado ya daina bayyana kansa a matsayin sarki, Gwamna Abba kuma ya sa a tsare shi.

A halin yanzun dai Sarki Sanusi II na zaune a babbar fadar Kofar Kudu yayin da Aminu Ado ke zaune a ƙaramar fadar Nasarawa, kowane na ganin shi ne Sarki.

NNPP ta yabawa Gwamnan Kano

A wani rahoton kuma NNPP reshen jihar Legas ta yabawa gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf kan dawo da Muhammadu Sanusi a kan sarautar Kano

Jam'iyyar mai kayan marmari ta kuma yabawa gwamnan kan yadda ya yi ƙoƙari wajen kiyaye martabar al'adun jihar Kano.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel