Yajin Aiki: ’Yan Kwadago Sun Rufe Asibiti a Kano, Marasa Lafiya Sun Shiga Damuwa

Yajin Aiki: ’Yan Kwadago Sun Rufe Asibiti a Kano, Marasa Lafiya Sun Shiga Damuwa

  • A yau Litinin kungiyoyin kwadagon NLC da TUC suka shiga yajin aiki saboda karin albashin ma'aikata a Najeriya
  • Yajin aikin ya jawo kulle ma'aikatun gwamnati daban daban a faɗin Najeriya inda ayyuka suka tsaya cak
  • A jihar Kano, kungiyar ta kulle asibitin Muhammadu Abdullahi Wase yanayin da ya jefa marasa lafiya cikin damuwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - A yau Litinin, 3 ga watan Yuni kungiyoyin kwadago suka shiga yajin aiki a Najeriya saboda rashin cimma matsaya kan karin albashin ma'aikata.

Kungiyar ta umurci dukkan ma'aikatun gwamnati su kulle saboda tilasta gwamnatin tarayya biya musu bukatu.

Asibitin Kano
Kungiyar kwadago ta rufe asibiti a Kano saboda yajin aiki. Hoto: SuleimanAbdullahi
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa kungiyar kwadago ta rufe asibitin koyarwa na Abdullahi Wase da ke Kano.

Kara karanta wannan

Yajin aikin kungiyoyin ƙwadago ya ɗauki zafi, an rufe ofishin ministan Abuja

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Halin da yajin aikin ya jefa asibitin MAWTH

Rahotanni sun tabbatar da cewa marasa lafiya a asibitin sun shiga damuwa bayan kulle asibitin da kungiyar kwadago ta yi.

Ma'aikatan lafiya sun watse sun bar marasa lafiya ba tare da masu kulawa da matsalolin da suke fama da su ba.

Yaushe likitoci za su dawo asibitin?

Marasa lafiya da suke kwance a asibitin sun ce a halin yanzu ba su san yaushe likitoci za su dawo duba su ba.

Hakan ya saka wasu daga cikin marasa lafiya masu jin dama-dama tafiya gida ba tare da bata lokaci ba.

Yajin aiki: Likitoci na aiki a boye

Wani babban ma'ikacin asibitin da ya bukaci a boye sunansa ya ce duk da yajin aikin suna duba marasa lafiya ta bayan fage.

Marasa lafiya da dama musamman wadanda suke fama da cututtuka masu tsanani sun koka kan rufe asibitin da kungiyar kwadago ta yi.

Kara karanta wannan

Yajin aiki: Likitoci a Kano sun watsawa kungiyar NLC kasa a ido

Gwamnati ta yi kira ga kungiyar NLC

A wani rahoton, kun ji cewa ministan yada labarai, Idris Muhammad ya yi kira ga kungiyar kwadago kan yajin aiki da ta fara a yau Litinin.

Ministan ya ce bai kamata kungiyar kwadago ta shiga yajin aiki ba tare lura da yadda kasar ke fama da matsanancin tattalin arziki ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng