Yayin da Ake Rigimar Sarautar Kano, Tsaro Ya Taɓarɓare, an Farmaki Gidan Shugaban APC

Yayin da Ake Rigimar Sarautar Kano, Tsaro Ya Taɓarɓare, an Farmaki Gidan Shugaban APC

  • Yayin da ake ci gaba da dambarwa kan sarautar Kano, wasu yan daba sun yi kokarin kutsawa gidan shugaban jam'iyyar APC a jihar
  • Rundunar ƴan sanda a jihar ta tabbatar da haka a cikin wata sanarwa da ta fitar a yau Lahadi 2 ga watan Yuni
  • Kakakin rundunar, Haruna Kiyawa ya ce sun yi nasarar dakile mamayar da ƴan daban suka yi a karamar hukumar Gwale

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Rundunar ƴan sanda ta tabbatar da dakile mamayar ƴan daba a gidan shugaban jam'iyyar APC, Abdullahi Abbas.

Rundunar ta ce yan daban sun yi yunkurin kutsawa gidan ne a ranar 31 ga watan Mayu da misalin karfe 6:00 na yamma.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun cafke wanda ya kashe 'yan NYSC a zanga zangar Buhari ya fadi zaben 2011

Yan sanda sun dakile yunkurin kai hari gidan shugaban APC a Kano
Tsaro yana kara tabarbarewa a Kano bayan yunƙurin kai hari gidan shugaban APC. Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa.
Asali: Facebook

Yan sanda sun dakile hari a Kano

Kakakin rundunar ƴan sanda a jihar, Haruna Abdullahi Kiyawa shi ya tabbatar da haka a shafin Facebook a yau Lahadi 2 ga watan Yuni.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kiyawa ya ce sun samu kiran gaggawa daga kwanan Chiranchi a karamar hukumar Gwale da ke jihar.

"Mun samu rahoton cewa matasa dauke da makamai suna jifan mutane da duwatsu yayin da suke kokarin shiga gidan shugaban APC."

- Haruna Kiyawa

Ƴan sanda sun dauki mataki kan lamarin

Kiyawa ya ce daga bisani rundunar ta kai ɗauki yankin inda ta tabbatar da zaman lafiya a wurin tare da yin gargadi ga jama'a wurin bin doka da oda.

Ya ce ana ci gaba da bincike yayin da aka gano fada ne tsakanin bangarori biyu masu gaba da juna da Abdul’Yassar Alias Jonny da Birbiri da Jinjiri Aljan ke jagoranta.

Kara karanta wannan

Kotu ta kori ƴan APC 25, ta hana su ayyana kansu a matsayin 'yan majalisa

Yan tauri sun fara tsorata ƴan Kano

A wani labarin, kun ji cewa mazauna jihar Kano musamman makwaftan fadar Sarkin Kano, sun koka kan yawaitar 'yan tauri a yankin fadar.

Idan ba a manta ba, mun ruwaito cewa 'yan tauri sun yi wa fadar Sarkin Kano tsinke domin ba da tsaro ga Muhammadu Sanusi II.

Daboon Dambazau, wani ma'abocin shafin X ya bayyana cewa ayyukan 'yan tauri a yankin ya jefa tsoro a zukatan jama'a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel