Yayin da Ake Batun Sauya Tsarin Mulki, Shettima Ya Fadi Babban Matsalar Najeriya

Yayin da Ake Batun Sauya Tsarin Mulki, Shettima Ya Fadi Babban Matsalar Najeriya

  • Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya magantu kan neman sauya tsarin mulkin Najeriya da wasu ke kira
  • Kashim ya ce babban matsalar kasar nan rashin shugabanci nagari ne ba maganar sauya tsarin mulki ba
  • Tsohon gwamnan Borno ya bayyana haka ne yayin wani taro a birnin Ilorin da ke jihar Kwara a yau Asabar 1 ga watan Yuni

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya bayyana babban abin da Najeriya ke bukata a yanzu.

Kashim ya ce matsalar kasar ba sauya tsarin gwamnati ba ne illa samar da shugabanci nagari.

Kashim Shettima ya magantu kan matsalolin Najeriya sabanin sauya tsarin mulki
Kashim Shettima ya kare Shugaba Bola Tinubu game da katsalandan a zabe. Hoto: Kashim Shettima.
Asali: Twitter

Shettima ta magantu kan matsalolin Najeriya

Kara karanta wannan

Abubuwan kunya 6 da suka faru da Gwamnatin Tinubu a cikin shekara 1

Shettima ya bayyana haka ne a yau Asabar 1 ga watan Yuni a birnin Ilorin na jihar Kwara yayin wani babban taro, cewar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan martani na Kashim na zuwa ne yayin da ake yada jita-jitar sauya tsarin yadda ake tafiyar da gwamnatin Najeriya, The Guardian ta tattaro.

"Dimukradiyya na samun ci gaba ne kadai idan aka samar da shugabanci nagari da kuma bin doka da oda."
"Bin tsarin fira minista ba shi ya ke nuna ci gaban dimukradiyya ba kamar yadda wasu ke tunani."
"Kasashe da dama sun ruguje ne saboda rashin bin doka da kuma kin bin gaskiya tare da cin amana."

- Kashim Shettima

Shettima ya kare Tinubu kan maganar zabe

Shettima ya kuma karyata cewa Shugaba Tinubu ya na katsalandan a harkokin zaben da ake gudanarwa a kasar.

Kara karanta wannan

Ana tsaka da rigimar sarautar Kano, Kwankwaso ya fadi abin da ke dagula Arewa

Ya kuma tabbatar da cewa Gwamnatin Tarayya ba ta taɓa amfani da ikonta ba wurin gallazawa ƴan adawa ba a shari'a daban-daban da suke yi.

Buhari ta taya Tinubu murna

A wani labarin, kun ji cewa tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya taya Shugaba Bola Tinubu murnan cika shekara daya a kan mulki.

Buhari ya roki ƴan Najeriya da su ci gaba da ba Tinubu goyon baya da hadin kai domin inganta rayuwar yan kasar.

Wannan na zuwa ne bayan shugaban ya cika shekara daya kan mulki da ƴan kasar ke kokawa kan halin da ake ciki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel