Abuja: AEDC Zai Datse Wutar Ma’aikatu 24 Na Gwamnatin Tarayya, Ya Ba da Sharaɗi

Abuja: AEDC Zai Datse Wutar Ma’aikatu 24 Na Gwamnatin Tarayya, Ya Ba da Sharaɗi

  • Kamfanin rarraba wutar lantarki na Abuja ya ba abokan huldarsa wa'adin awanni 72 su biya kudin wuta ko su kwana a duhu
  • AEDC ya ce zai datse wutar ma'aikatun gwamnatin tarayya guda 24 da kuma jihohin Kogi da Neja kan rashin biyan kudin wutar
  • Kamfanin AEDC ya bayyana cewa biyan kudin wutar na da matukar muhimmanci ga dorewar samar wuta ba tare da tsaiko ba

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Kamfanin rarraba wutar lantarki na Abuja ya yi barazanar yanke wutar abokan huldarsa da suka gaza biyan kudin wutar da suka sha nan da 3 ga watan Yuni.

AEDC ya yi magana kan kudin wutar lantarki
Abuja: Kamfanin AEDC ya aika sako ga abokan huldarsa kan biyan kudin wuta.
Asali: UGC

Wannan barazanar na kunshe a cikin wata sanarwa da shugaban kamfanin, Victor Ojelabi ya fitar a ranar Juma'a, 31 ga watan Mayu.

Kara karanta wannan

Taken Najeriya: Tinubu ya yi karin haske kan hikimar komawa tsohon taken kasa

Kamfanin AEDC ya ba abokan hulda wa'adi

Channels TV ya rahoto Victor Ojelabi ya bayyana cewa ko dai abokan hulda su biya kudin wutar lantarkin da suke sha ko kuma mu yanke wutar su.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar Victor Ojelabi:

"Kamfanin rarraba wutar lantarki na Abuja na kira ga abokan hulda da su biya kudin da ake bin su ko kuma su rika kwana a duhu.
"Muna ba abokan hulɗa wa'adin awa 72 su biya kudin da ake bin su zuwa Litinin, 3 ga watan Yuni, 2024 ko kuma mu datse wutar."

Muhimmancin biyan kudin wutar lantarki

Kamfanin rarraba wutar ya nuna muhimmancin biyan kudin wuta a kan lokaci wanda hakan zai taimaka masa wajen biyan bukatun abokan huldarsa ba tare da tsaiko ba.

"Biyan kudin wuta na da matukar muhimmanci ga dorewar samar da ayyukan AEDC, wannan zai sa a samu wuta ba dauke wa."

Kara karanta wannan

Kano: Adadin wadanda suka mutu a harin masallaci ya karu, sanata ya ba da N15m

AEDC na bin ma'aikatun gwamnati bashi

Kamfanin na AEDC ya ce zai datse wutar ma'aikatun gwamnatin tarayya guda 24 da kuma jihohin Kogi da Neja kan rashin biyan kudin wutar lantarki, in ji rahoton The Nation.

Kamfanin na bin ma’aikatu da hukumomi daban-daban da suka hada da ma’aikatar kudi ta tarayya bashin sama da Naira biliyan 100, kamar yadda ya yi ikirari.

TCN ya gyara matsalar wutar Najeriya

A wani labarin, mun ruwaito cewa kamfanin kula da wutar lantarki na Najeriya, (TCN) ya yi aiki tuƙuru, ya gyara matsalar wutar da aka shiga a Najeriya.

A kwanakin nan ne aka samu lalacewar tushen wutar lantarki na Najeriya, lamarin da ya jawo daukewar wutar a kasar, sai dai TCN ya ce ya shawo kan matsalar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.