Alhazan Yobe 1,332 Sun Karbi N179.8m Daga Gwamnatin Jihar

Alhazan Yobe 1,332 Sun Karbi N179.8m Daga Gwamnatin Jihar

  • Gwamnatin jihar Yobe karƙashin Gwamna Mai Mala Buni ta cika alƙawarin da ta ɗauka na tallafawa alhazan jihar 1,332
  • Shugaban hukumar jin daɗin alhazai na jihar, Alhaji Mai Aliyu ya ce kowane mutum ɗaya daga cikin mahajjatan ya samu alawus na N135,000
  • Ya ce a halin yanzun an kammala kwashe alhazan jihar zuwa Madinah kuma galibi sun kama hanya zuwa Makkah sauran kaɗan ya rage

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Yobe - Hukumar Alhazai ta jihar Yobe ta ce ta biya tallafin Naira miliyan 179.8 da Gwamnatin Mai Mala Buni ya amince a rabawa maniyyata 1,332 na jihar.

Gwamma Mai Mala Buni ya bai wa maniyyatan wannan tallafi ne domin taimaka masu su gudanar da aikin hajjin bana 2024 cikin farin ciki da walwala.

Kara karanta wannan

Gwamna ya sa tukuicin N25m ga duk wanda ya taimaka aka kama waɗanda suka kashe sojoji

Gwamna Mai Mala Buni.
Gwamnatin Yobe ta cika alƙawari, ta bai wa alhazan jihar tallafi Hoto: Mai Mala Buni
Asali: Twitter

Shugaban hukumar alhazan Yobe, Alhaji Mai Aliyu ne ya bayyana haka a lokacin da yake yiwa gwamnan karin bayani kan jigilar maniyyatan zuwa ƙasa mai tsarki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Buni ya tallafawa alhazai

Ya ce kowane mahajjaci ya samu N135,000 na alawus alawus na tafiya kamar yadda gwamna ya bayar da umarni, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

A cewarsa, dukkan maniyyatan da jami’an hukumar jin daɗin alhazai ta jihar, an kammala jigilarsu zuwa kasar Saudiyya.

"Sun sauka lafiya a Madina, birni na biyu mai tsarki don gudanar da ayyukan ibada da ziyarce-ziyarce, kuma a yanzu sun wuce Makkah, in ban da ‘yan kadan da ke Madina har yanzu,” Inji Aliyu.

Shugaban ya bayyana cewa hukumar ta samu damar kama otal-otal na kusa, waɗanda babu nisa tsakani da masallatai masu tsarki a Madina da Makkah. 

Kara karanta wannan

Babu alamun warware rikicin sarautar Kano bayan ganawar Gwamna Abba da NSA

Ya ce dukkan maniyyatan suna cikin koshin lafiya kuma suna yiwa gwamna da gwamnatin jihar Yobe addu'ar fatan alheri, Allah ya karawa jihar Yobe da Nijeriya zaman lafiya.

Gwamna Buni ya yaba da aikin jigila

Gwamna Buni ya yabawa hukumar da kamfanonin jiragen sama bisa yadda suka tabbatar da an kammala jigilar alhazai a kan lokaci.

Ya kuma bukaci hukumar ta kula da alhazan jihar Yobe yadda ya kamata kuma ta bai wa walwala da jin daɗinsu fifiko, Daily Trust ta ruwaito.

Gwamna Buni ya yi addu’ar Allah ya karbi wannan ibada ta alhazan da kuma addu’o’in da suke yi sannan Allah ya dawo da su gida lafiya.

Da gaske EFCC ta fara binciken Kwankwaso?

A wani rahoton kuma shugaban NNPP na jihar Kano ya musanta rahoton cewa hukumar EFCC ta taso Kwankwaso kan wasu kuɗaɗen kamfe.

Hashimu Dangurawa ya ce rahoton ƙarya ne kuma wasu maƙiyan Kwankwaso suka kirkiro shi domin ɓata masa suna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel