Jam'iyyar NNPP Ta Yabawa Gwamna Abba Kan Dawo da Sanusi II, Ta Fadi Kokarin da Ya Yi

Jam'iyyar NNPP Ta Yabawa Gwamna Abba Kan Dawo da Sanusi II, Ta Fadi Kokarin da Ya Yi

  • Jam'iyyar NNPP reshen jihar Legas ta yabawa gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf kan dawo da Muhammadu Sanusi a kan sarautar Kano
  • Jam'iyyar ta kuma yabawa gwamnan kan yadda ya yi ƙoƙari wajen kiyaye martabar al'adun jihar Kano
  • Jam'iyyar ta bayyana cewa dawo da tsohon gwamnan na babban bankin Najeriya (CBN) abu ne mai kyau domin kiyaye martabar al'adun jihar

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Jam’iyyar NNPP reshen jihar Legas ta yabawa gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, bisa ƙoƙarinsa na kiyaye martabar al’adun gargajiyar jihar.

Jam'iyyar ta kuma yabawa gwamnan kan sake naɗa Muhammadu Sanusi II a matsayin Sarkin Kano.

NNPP ta yabawa Gwamna Abba Kabir Yusuf
Jam'iyyar NNPP ta yabi Gwamna Abba kan dawo da Sanusi II sarauta Hoto: Abba Kabir Yusuf, Sanusi Lamido Sanusi
Asali: Facebook

NNPP ta yabawa Gwamna Abba

Sakataren yaɗa labaran jam’iyyar na jihar, Richard Benson ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Legas ranar Juma’a, cewar rahoton jaridar Vanguard.

Kara karanta wannan

Sanusi II vs Aminu Ado: An ba Gwamna Abba lakanin warware rikicin sarautar Kano

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Richard Benson ya ce mayar da tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), a matsayin Sarkin Kano na 16 abu ne mai kyau domin kiyaye al’adun jihar.

Sakataren ya kuma yabawa tsohon gwamnan jihar kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar NNPP a zaɓen 2023, Rabi'u Musa wankwaso, bisa ƙoƙarinsa na tabbatar da an kiyaye al'adun Kano, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar.

Me NNPP ta ce kan Gwamna Abba?

"Mu jam’iyyar NNPP reshen jihar Legas, muna yabawa ƙoƙarin mai girma gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, da jagoranmu na ƙasa Rabi’u Musa Kwankwaso da ɗaukacin majalisar dokokin Kano wajen ganin an kiyaye al'adun Kano bisa gaskiya."
"Hakan ya bayyana ƙarara a Kano domin nuna cewa al'adun gargajiyar birnin Kano an mutunta su sannan mafi yawan mutane suna farin cikin ganin cewa al'adunsu na nan daram yadda suke."

Kara karanta wannan

Ana tsaka da rikicin sarautar Kano, jam'iyyar Kwankwaso ta aike da saƙo ga Bola Tinubu

- Richard Benson

Ya ƙara da cewa a yanzu jihar na samun gagarumin sauyi a harkokin mulki saboda jajircewar Gwamna Abba Kabir Yusuf.

An ba Gwamna Abba shawara

A wani labarin kuma, kun ji cewa wata ƙungiya mai suna 'Concerned Citizens of Kano' ta caccaki Gwamna Abba Kabir Yusuf kan rushe masarautun Kano.

Ƙungiyar ta buƙaci gwamnan da ya gaggauta fitowa ya nemi afuwar al'ummar jihar Kano saboda abun kunyar da ya jawo musu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel