Babu Alamun Warware Rikicin Sarautar Kano bayan Ganawar Gwamna Abba da NSA
- Ga dukkan alamu ganawar Gwamna Abba Kabir da Nuhu Ribaɗu ba ta lalubo hanyar warware rikicin sarautar Kano ba
- Gwamna Abba ya ce ya ziyarci mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan tsaro ne domin masa bayani kan halin da ake ciki a jiharsa
- Sai dai dukkan ɓangarorin biyu ba su bayyana wani mataki da aka ɗauka a taron da nufin warware rikicin sarautar ba
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kano - A ƴan kwanakin nan Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya gana da mai baiwa shugaban ƙasa shawara kan harkikin tsaro, Nuhu Ribaɗu.
Ana ganin wannan ziyara da gwamnan ya kai wa Ribaɗu ba za ta rasa nasaba da dambarwar da ta ƙi ci kuma ta ƙi cinyewa kan sarautar Kano ba.
Kamar yadda Leadership ta ruwaito, alamu sun nuna an tashi wannan ganawa ba tare da lalubo hanyar warware rikicin sarautar Kano ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A halin yanzun dai Muhammadu Sanusi II da Alhaji Aminu Bayero kowa na ikirarin shi ne Sarkin Kano, lamarin da ya kawo ruɗani a tsakanin al'umma.
Dalilin rikicin sarauta a Kano
Gwamnatin jihar Kano ta zartar da wata doka da ta soke masarautu hudu, wadanda gwamnatin Abdullahi Ganduje ta kirkiro tun a 2019 tare da mayar da masarauta ɗaya.
Jim kaɗan bayan haka kuma Gwamnatin Abba Kabir ya mayar da Muhammadu Sanusi kan karagar sarkin Kano.
Da farko gwamnatin jihar ta zargi Nuhu Ribadu da hannu wajen dawo da Aminu Bayero jihar amma daga baya ta dora laifin a kan jam’iyyar APC da Ganduje.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yanke zuwa ya zauna da Malam Nuhu Ribadu ranar Alhamis da ta gabata.
NSA da Abba sun gaza warware matsalar
Sai dai ofishin NSA ya ki bayyana sakamakon ganawar da aka kwashe sa’o’i ana yi tsakanin jiga-jigan biyu.
Sanarwar da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature ya fitar kuma aka rabawa manema labarai a Kano ranar Alhamis ba ta yi magana kan sakamakon taron ba.
A cewar Bature taron wanda ya dauki sama da sa’a guda, ya maida hankali ne kan batun rusa masarautu guda biyar da majalisar dokokin jihar Kano ta yi.
Sanarwan ta tattaro Gwamna Abba na cewa:
"Mun yi tattaunawa ta fahimtar juna tsakanina da mai ba da shawara kan tsaron ƙasa, aikinsa na da matuƙar muhimmanci ga zaman lafiyar kasa. Hakan ya sa na yi masa bayani kan abubuwan da ke faruwa a Kano."
Huɗubar Sanusi II a masallacin Jumu'a
A wani rahoton kuma Sarki Muhammadu Sanusi II ya jagoranci sallar Jumu'a a babban masallacin Ƙofar Kudu a Kano kuma ya yi huɗuba kan imani da Allah.
Basaraken ya bayyana cewa babu wanda zai ja da hukuncin Allah, inda ya ƙara da cewa komai ka ga ɗan adam ya samu ko ya rasa daga Allah ne.
Asali: Legit.ng