Kano: Jawabin Karshe da Sanusi II Ya yi Kafin Maida Shi Gadon Sarautar Dabo

Kano: Jawabin Karshe da Sanusi II Ya yi Kafin Maida Shi Gadon Sarautar Dabo

  • Muhammadu Sanusi II ya shafe shekaru hudu bai da kasa bayan gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta tunbuke shi
  • Mai Martaban ya rasa rawaninsa ne a shekarar 2020 sai ga shi ya dawo kan karaga bayan an yi canjin gwamnati a Kano
  • Sanusi II wanda masanin tattalin arziki ne yana wajen taro a garin Fatakwal lokacin da aka fahimci zai koma sarauta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Kano - A makon da ya gabata ne aka tabbatar da Muhammadu Sanusi II a matsayin sabon sarkin Kano kuma Sarki na 16.

Majalisar dokokin jihar Kano ta soke dokar masarauta ne a lokacin Muhammadu Sanusi II yana halatar taro a jihar Ribas.

Muhammadu Sanusi II
Muhammadu Sanusi II ya yi magana a Ribas kafin sake nada shi Sarkin Kano Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Muhammadu Sanusi II ya samu labari a Ribas

Kara karanta wannan

Ana tsaka da rikicin sarautar Kano, Sarki Muhammadu Sanusi II ya yi nadin farko

Leadership ta ce lokacin da labari ya fara yawo, Mai martaba ya gabatar da jawabi kan tattalin arziki a can garin Fatakwal.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A jawabin da ya yi, Muhammadu Sanusi II ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta sausauta a wajen kakabawa jama’a haraji.

Mai girma Similayi Fubara ya gayyato tsohon gwamnan babban bankin CBN ya tattauna a kan zancen zuba hannun jari.

Kiran Sanusi II ga gwamnatin tarayya

BBC ta rahoto Sarkin ya na kira ga gwamnatin Bola Tinubu ta guji matsawa al’umma a lokacin da ake cikin matsalar tattali.

Masanin tattalin ya tsakuro maganar tsohuwar Firaministar Birtaniya, Margaret Thatcher, wanda ta soki yawan tatsar haraji.

A ra’ayin Margaret Thatcher, babu wata kasa a duniya da ta ke cigaba ta hanyar matsawa al’ummarta da yawan karbar haraji.

Sai dai Khalifa Sanusi II bai soki lamarin gaba daya ba, ya nuna haraji yana da muhimmanci idan gyara kasar ake so.

Kara karanta wannan

Ana tsaka da ruɗanin hukuncin kotuna 2, jigon NNPP ya yi magana kan naɗin Sarkin Kano

Sanusi II yake cewa bai kamata gwamnatin Najeriya ta kwallafa rai da haraji har abin ya zama ana neman riba da jinin talaka ba.

Business Day ta ce Basaraken ya ba gwamna Simi Fubara shawarar ya rabu da kudin mai, ya tsaya ya yi abin da za a rika tuna shi.

Gwamnatin Bola Tinubu tayi suna wajen laftawa jama’a haraji tun da ta karbi mulki.

Sakon Dan Sarauniya ga Muhammadu Sanusi II

Ana da labari cewa tsohon ‘dan takaran gwamnan jihar Kano ya fadi abin da ya jawowa Muhammadu Sanusi II matsala a baya.

Muaz Magaji ya ce idan Muhammadu Sanusi II sarauta ya dawo yayi, suna bayansa kuma za su yake shi idan ya kutsa harkar siyasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng