Tinubu Ya Burma Matsala, Lauyoyi Za Su Maka Shi a Kotu Kan Wani Kuskuren da Ya Tafka
- Da alamu shugaban kasa, Bola Tinubu ya shiga matsala kan sauya taken Najeriya da ya yi a dai-dai wannan lokaci
- Kungiyar lauyoyi ta ALDRAP ta shirya maka shugaban a kotu kan rashin bin tsari wurin tabbatar da dokar a Najeriya
- Wannan na zuwa ne bayan Tinubu ya rattaba hannu kan dokar sauya taken Najeriya wanda ƴan kasar suka kushe
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Kungiyar lauyoyi ta ALDRAP za ta maka Shugaba Bola Tinubu a gaban kotu.
ALDRAP da kungiyoyin kare hakkin al'umma za su maka shugaban a kotu kan sauya taken Najeriya.
Taken Najeriya: Musabbabin maka Tinubu a kotu
Sakataren kungiyar ALDRAP, Tonye Jaja shi ya tabbatar da haka a yau Juma'a 31 ga watan Mayu, cewar TheCable.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jaja ya ce ba a bi tsari ba wurin ɗaukar matakin da Majalisar ta yi wanda ya saba ka'idar tabbatar da doka, Daily Post ta tattaro.
"Ba a bi tsari ba wurin tabbatar da dokar kamar yadda sashen 60 na kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 ya tanadar."
"Kuma ba a gayyaci jama'a ba wurin jin ra'ayinsu da kuma gudunmawarsu kamar yadda aka yi a 1978."
"Babu wata takarda da shugaban kasa ya tura zuwa ga shugabannin Majalisun gida biyu."
- Tonye Jaja
Wannan na zuwa ne bayan Tinubu ya sauya taken Najeriya daga "Arise O Compatriot" zuwa "Nigeria We Hail Thee" a wannan mako da muke ciki.
Ƴan Najeriya da dama sun kushe wannan mataki na Tinubu musamman a daidai lokacin da ake cikin wani irin hali.
Gwamanti ta bukaci a haddace taken Najeriya
A wani labarin, kun ji cewa Hukumar wayar da kan jama'a a Najeriya (NOA) ta bukaci a haddace sabon taken Najeriya cikin kwanaki uku.
NOA ta ba da wannan sanarwa musamman ga jami'anta da ke duka ƙananan hukumomi 774 a fadin Najeriya.
Hakan ya biyo bayan sauya taken Najeriya da Tinubu ya yi daga "Arise O Compatriot" zuwa "Nigeria We Hail Thee" a wanna mako.
Asali: Legit.ng