Ana Fama da Rikicin Sarautar Kano, Gwamnan APC Ya Naɗa Sababbin Sarakuna
- Gwamnan jihar Kebbi, Dakta Nasir Idris Ƙauran Kwandu ya naɗa sababbin hakimai da dagattai guda 14 a wasu sassan jihar
- Kwamishinan kananan hukumomi da masarautu, Garba Umar Dutsinmari ne ya bayyana haka a wata sanarwa ranar Alhamis
- Ya bayyana cewa naɗin sarakunan ya fara aiki ne tun ranar 28 ga watan Mayu, 2024, inda ya jero sunayen waɗanda gwamnan ya naɗa
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kebbi - Gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris ya amince da nadin sababbin hakimai tara da kuma dagattai guda biyar a jihar.
Nadin nasu na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun kwamishinan kananan hukumomi da masarautu, Garba Umar Dutsinmari.
Gwamnan Kebbi ya sanar da nadin sarauta
Kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito, sanarwar naɗe-naɗen sarakunan ta shiga hannun manema labarai a Birnin Kebbi a jiya Alhamis, 30 ga watan Mayu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kwamishinan kananan hukumomi da masarautu na jihar Kebbi ya ce naɗin sarakunan ya fara aiki ne tun ranar 28 ga watan Mayu, 2024.
Jerin sababbin hakimai 9 a Kebbi
Sababbin hakiman da Gwamna Nasir Idris ya naɗa su ne:
1. Alhaji Muhammad Bello Koko - Sabon hakimin Koko
2. Alhaji Muhammad Kabir Hassan Kwaido - Sabon hakimin Yola (Lamnen Yola).
3. Honorabul Tukur Yalli - Sabon hakimin Bakuwai
4. Hussani Marafa (Sarki Yamman Alelu) - Sabon hakimin Alelu
5. Bello Hassan - Sabon hakimin Yeldu (Mai Arewa Yeldu)
6. Yakubu Hassan Geza - Sabon hakimin Geza
7. Muhammad Nura Sauwa (Sarkin Yamman Sauwa) - Sabon hakimin Sauwa.
8. Alhaji Sa’adu Sauwa - Sabon hakimin Ƙauran Sani
9. Alhaji Kabiru Yakubu mai Arewa - Sabon hakimin Mai Arewan Sarkan.
Gwamna ya naɗa dagattai a Kebbi
Ƙauran Gwandu ya kuma naɗa dagattai na kauyuka biyar wanda suka haɗa da Mai Yamman Rafi Atiku da ke gundumar Nassarawa a Birnin Kebbi, Alhaji Abdu Mai Bulo, sabon dagacin kauyen.
Sauran ƙauyukan da gwamnan ya naɗa masu dagattai sun hada da Gawasu, Guwaba Gabas, Kawate da Wahannu.
NNPP ta yabawa gwamnatin Bola Tinubu
A wani rahoton kuma jam'iyyar NNPP mai kayan maramari ta yabawa shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu a lokacin da yake cika shekara ɗaya a mulki.
Uban NNPP Boniface Aniebonam ya ce tun asali Bola Tinubu ya karɓi kasar a lokacin da matsaloli suka yi mata katutu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng