Rusau a Kasuwar Lagos: Zuciyar Dattijuwa Ta Buga, Ta Rasu Bayan Rasa N50m a Shago

Rusau a Kasuwar Lagos: Zuciyar Dattijuwa Ta Buga, Ta Rasu Bayan Rasa N50m a Shago

  • Wata baiwar Allah, Alhaja Iyabo ta rasa ranta bayan zuciyarta ta buga lokacin da ta tabbatar da tafka asara a rushe kasuwar Alaba Rago inda 'yan kasuwa da yawa suka yi asara
  • Rahotanni sun ce matar da yi asarar akalla N50m domin ta tattare kudin kasuwancinta a cikin shagonta dake kasuwar kamar yadda wasu yan kasuwa suka yi
  • Gwamnatin Lagos dai ta bayyana cewa ta ba ‘yan kasuwar sanarwar fara rushe shagunansu, amma masu shaguna a kasuwar sun musanta hakan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Lagos - An shiga takaici bayan zuciyar wata ‘yar kasuwa, Alhaja Iyabo ya buga, wanda ya yi sanadiyyar rasuwarta a jihar Lagos.

Kara karanta wannan

Diyar Ado Bayero ta turawa Tinubu da Abba sako, tayi zancen rigimar masarautar Kano

Zuciyar marigayiyar ya buga ne bayan ta tafka asara a rusau din da gwamnatin jihar Lagos ke yi a kasuwar Alaba Rago.

Gwamnan Lagos
Zuciyar 'yar kasuwar da ta rasa N50m ya buga a Lagos Hoto: The Lagos State Government
Asali: Facebook

Daily Trust ta tattaro cewa wannan baiwar Allah ta rasa akalla N50 da ta ajiye a asusunta dake cikin shagon da aka ruguje.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnatin Lagos ta sanar da fara rusau

Rahotanni sun bayyana cewa gwamnatin jihar Lagos ta sanar da ‘yan kasuwar Alaba Rago cewa za ta fara rushe kasuwar, saboda haka su tashi.

Shugabannin kasuwar sun bayyana cewa gwamnati ta fara rushe kasuwar inda a yanzu aka tabbatar da rasa akalla N50b, kamar yadda Nairaland ta wallafa.

Daga cikin kayan da aka rasa a kasuwar akwai shinkafa, wake, da dabbobin ‘yan kasuwar ciki har da Alhaja Iyabo da ta rasa ranta.

‘Yan kasuwa sun karyata gwamnatin Lagos

Kara karanta wannan

'Abin kunya': NBA ta soki Lauyoyi da Masu shari'a kan dambarwar masarautar Kano

Wasu daga ‘yan kasuwar Alaba Rago kamar shugaban masu sayar da shanu, Ibrahim Hamad Namari, ya ce babu wata sanarwa daga gwamnati kan fara rushen-rushen.

Ya ce an bawa wani bangare na kasuwar sanarwar cewa za a fara rusa, amma ba a bayyana ainihin rana ko wuraren da za a rushe ba.

Mallam Ibrahim Hamad Namari, ya ce bayan sun samu labarin fara rushe-rushen suka dunguma kasuwar, inda suka tarar da dimbin asara.

Maniyyacin Lagos ya rasu a Saudiyya

A baya mun kawo muku labarin yadda wani maniyyacin aikin hajjin bana daga jihar Lagos, Idris Olosogbo ya riga mu gidan gaskiya bayan ya isa kasa mai tsarki.

Marigayin ya rasu ne bayan ya dawo daga dawafi, kamar yadda babban sakataren hukumar jin dadin alhazan jihar Lagos Saheed Onipede ya shaida.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Online view pixel