Dubun Baleri Ta Cika: Sojojin Kasar Nijar Sun Kwamushe Ɗan Ta’addan da Ake Nema

Dubun Baleri Ta Cika: Sojojin Kasar Nijar Sun Kwamushe Ɗan Ta’addan da Ake Nema

  • Sojojin jamhuriyar Nijar sun kama kasurgumin ɗan bindiga da ake kira Baleri yayin da zai kai mummunan hari
  • A kwanakin baya sojojin Najeriya suka wallafa sunan Baleri cikin manyan yan ta'addan da suke nema ruwa a jallo
  • Baleri ya kasance cikin shugabannin yan ta'adda a yankunan Nijar da Najeriya da suke kashe mutane ba dare ba rana

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Nijar - Rundunar sojin Jamhuriyar Nijar ta tabbatar da kama kasurgumin ɗan ta'adda da aka fi sani da Baleri.

Baleri na cikin yan ta'addan da suka fitini yankin Arewacin Najeriya musamman Arewa maso yammacin kasar.

Baleri
Sojoji sun kama Baleri a Nijar. Hoto: Basheer Maradoon
Asali: Facebook

Jaridar Aminiya ta tabbatar da cewa an kama Baleri ne a yayin da yake kokarin kai wani hari shi da yaransa a yankin Maraɗi.

Kara karanta wannan

Sojojin Najeriya sun kashe shugabannin yan ta'adda bayan fafatawa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A ina sojoji suka kama Baleri?

Rundunar sojin Nijar ta sanar da cewa ta kama Baleri ne a yankin Rigar Kowa Gwani da ke bangaren Gidan Rumji a jihar Maraɗi.

Sojojin runduna ta musamman da ke aiki karkashin Operation Farautar Bushiya ne suka kama dan ta'addan a kudancin Maradi.

Baleri ya shirya kai hari a Nijar

Rundunar sojin ta ce ta kama kasurgumin ɗan bindigar ne a lokacin da yake tsaka da tattaunawa cikin wani gungun yan bindiga, rahoton the Guardian Nigeria

Sannan rundunar ta kara da cewa ana kyautata zaton cewa yan bindigar yaransa ne kuma suna kitsa yadda za su kai hari ne a lokacin.

Sojoji suna neman Baleri ruwa a jallo

Tun bayan bayyanar ayyukan ta'addancin da Baleri ke aikatawa rundunar sojin Najeriya ta fara nemansa ruwa a jallo.

Rundunar ta sanya sunan Baleri a lamba ta 40 ciki yan ta'addan da ake nema ruwa a jallo tare da sanya kyauta ga duk wanda yasa aka gano shi.

Kara karanta wannan

Sojoji sun gano gidan da yan bindiga ke boye makamai, an kama mata da miji

Yan bindiga sun kai hari Aba

A wani rahoton, kun ji cewa wasu miyagun ƴan bindiga sun kai farmaki kan sojojin Bataliya ta 144 da ke garin Aba, cibiyar kasuwancin jihar Abia suna tsaka da gudanar da aikinsu.

Ana fargabar ƴan bindigan waɗanda suka kai harin cikin wata mota ƙirar SUV sun hallaka sojoji uku a yayin farmakin da suka kai musu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng