‘Daɗi Zai Biyo Baya’ Masana Sun Fadi Dalilin Goyon Bayan Tsare Tsaren Tinubu

‘Daɗi Zai Biyo Baya’ Masana Sun Fadi Dalilin Goyon Bayan Tsare Tsaren Tinubu

  • Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya cigaba da kirkiro sababbin tsare-tsaren da suke jefa al'umma cikin kuncin rayuwa
  • Gwamnatin Bola Tinubu ta sha bayyanawa yan Najeriya cewa ko da za a sha wahala a halin yanzu to tabbas sauki zai zo daga baya
  • Legit ta tattauna da Muhammad Ibrahim domin jin yadda yake ganin maganar da masanan suka yi wajen kara hakuri da mulkin Bola Tinubu

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Nigeria - Tun farkon fara mulki shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya fara kirkiro tsare-tsaren da suka jefa al'umma cikin tasko.

Duk da kokarin da gwamnatin ta yi wajen bayyanawa yan Najeriya cewa ta dauki matakan ne domin inganta kasar hakan bai yi tasiri ba.

Kara karanta wannan

Taken Najeriya: Tinubu ya yi karin haske kan hikimar komawa tsohon taken kasa

Shugaba Tinubu
Masana sun goyi bayan tsauraran matakan Bola Tinubu. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Wani masani ya tabbatar wa jaridar the Cable cewa matakan da gwamnatin ta dauka za su kai Najeriya kan tudun tsira.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsare-tsaren da Tinubu ya kawo

Cikin tsare-tsare masu tsauri da Tinubu ya kawo akwai cire tallafin man fetur da ya yi a ranar 29 ga watan Mayun shekarar 2023.

Haka zalika a ranar 3 ga watan Afrilu shugaban kasar ya kara kudin wutar lantarki ga yan layin Band A.

Karin haske daga masana

Wani masanin tattalin arziki, Muda Yusuf ya ce duk da cewa tsare-tsaren sun haifar da wahalar rayuwa ga talakawa amma suna da amfani.

Muda Yusuf ya ce dole ne yan Najeriya su kara hakuri da juriya domin tabbatar da tsare-tsaren sun kawo cigaba a nan gaba kadan.

Haka zalika wani masanin tattalin arziki, Ayokunle Olubunmi ya tabbatar da cewa duk da matsalolin da ake fama dasu a gaba za a samu sauki.

Kara karanta wannan

Tinubu ya tura sako ga shugabannin Arewa, tare da barazanar korar masu mukamai

Muda Yusuf ya yi kira ga Tinubu

Duk da cewa masanin ya goyi bayan gwamnatin, ya ce dole ta saka gaggawa wajen daukan matakan da za su rage radadin da tsare-tsaren suka jawo.

Ya ce shekarar farko da fara gyaran an sha wahala sosai saboda haka ya kamata a rika kawo dauki da wuri.

Legit ta tattauna da Muhammad Ibrahim

Wani mazaunin jihar Kano Muhammad Ibrahim ya zantawa Legit cewa lallai a matsayinsa na dan kasa maganar masanan ba ta kama hankalinsa ba.

Ya ce an sha fadin haka a kan gwamnatocin da suka gabata amma haka suke wucewa ba tare da samar da wata mafita ga al'umma ba.

Buhari ya taya Tinubu murna

A wani rahoton, kun ji cewa Muhammadu Buhari ya taya shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu murnar cika shekara ɗaya a kan madafun iko a Najeriya.

Tsohon shugaban ƙasar ya yi kira ga ƴan Najeriya su goyi bayan gwamnatin Tinubu a koƙarinta na kawo ci gaban ƙasa a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng