Yadda Tinubu Ya Cika Burin da Ya Dauka a 2022, Ya Dawo da Tsohon Taken Najeriya

Yadda Tinubu Ya Cika Burin da Ya Dauka a 2022, Ya Dawo da Tsohon Taken Najeriya

  • Abin da da yawan mutane ba su sani ba game da dawo da tsohon taken Najeriya shi ne; Tun a 2022 Shugaba Bola Tinubu ya ci buri kan hakan
  • A wata hira da aka yi da shi a bikin zagayowar ranar samun ‘yancin Najeriya a 2022, Tinubu ya ce zai dawo da tsohon taken kasar
  • Taken Najeriya da aka dawo amfani da shi a yanzu shi ne ‘Nigeria, We Hail Thee’ wanda ya maye gurbin taken 'Arise, O Compatriots’ na 1978

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

A ranar Laraba ne shugaban kasa Bola Tinubu ya rattaba hannu kan kudirin dokar sake dawo da tsohon taken Najeriya na ‘Nigeria, We Hail Thee’.

Kara karanta wannan

Taken Najeriya: Hadimin tsohon shugaban kasa ya caccaki Tinubu a karon farko

Burin Tinubu game da tsohon taken Najeriya
Tinubu ya na da burin dawo da tsohon taken Najeriya tun a 2022. Hoto: @officialABAT
Asali: Facebook

Matakin da shugaban ya dauka ya zo ne sa’o’i kadan bayan majalisar dattijai ta zartar da kudirin a yayin wani taron jin ra’ayin jama’a.

"An yi garaje a sauya taken" - AGF

Tinubu ya amince da kudirin ne duk da kiran da Lateef Fagbemi, babban lauyan gwamnatin tarayya (AGF) kuma ministan shari’a ya yi, in ji rahoton Arise News.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lateef Fagbemi ya ce ya kamata a bi matakai da kuma gabatar da babban tsari kafin a sauya taken kasar.

Taken Najeriya da aka dawo amfani da shi a yanzu shi ne ‘Nigeria, We Hail Thee’. Taken da aka rika amfani da shi tun 1978 shi ne 'Arise, O Compatriots’.

Tinubu na da burin sauya taken Najeriya

Sai dai kuma wani rahoton waiwaye da jaridar The Cable ta wallafa ya nuna cewa Tinubu ya ci burin dawo da tsohon taken Najeriya tun ma kafin ya zama shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Tsohuwar minista ta fusata, ta ce ba za ta komawa sabon taken Najeriya ba

A wata hira da aka yi da shi a lokacin bikin zagayowar ranar samun ‘yancin kai a Najeriya a shekarar 2022, Tinubu ya nuna fifikon sa ga tsohon taken fiye da na yanzu.

Ya ce tsohon taken "ya fi siffantamu da kyau" kuma ya ƙara da cewa "idan har na samu dama, zan dawo da taken ƙasarmu na farko".

Wani shafin YouTube mai suna Matters of Heritage ne ya wallafa bidiyon hirar da aka yi da Shugaba Bola Tinubu.

Tsohon taken Najeriya: Mutane sun fusata

A wani labarin, mun ruwaito cewa dawo da tsohon taken Najeriya ya fusata 'yan Najeriya, inda da yawa ke zargin gwamnatin tarayya da mayar da hankali kan abin da bai shafi talaka ba.

Legit ta tattaro muku ra'ayoyin daban-daban da yan Najeriya suka bayyana a kafafen sada zumunta kan sabon taken kasar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel