Gwamnatin Tinubu Na Bayar da Tallafin N250,000 Ga 'Yan Najeriya? Gaskiya Ta Bayyana

Gwamnatin Tinubu Na Bayar da Tallafin N250,000 Ga 'Yan Najeriya? Gaskiya Ta Bayyana

  • Wasu rahotanni da aka yaɗa a yanar gizo sun bayyana cewa gwamnatin APC na bayar da tallafin N250,000 ga dukkanin ƴan Najeriya
  • An yi amfani da hoton Zainab Ahmed, tsohuwar ministar kuɗi, kasafin kuɗi da tsare-tsare ta ƙasa, a wasu daga cikin rahotannin da aka yaɗa kan bayar da tallafin
  • Wani dandali na bincikar gaskiya ya binciki iƙirarin tare da bayyana sakamakon da ya samu a cikin wani rahoto da aka buga kwanan nan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Wani shafin Facebook mai suna 'Jobs and Travels' ya sanya wani rubutu inda ya bayyana cewa akwai tallafin N250,000 da gwamnatin APC ta ƙaddamar ga ɗaukacin ƴan Najeriya.

Kara karanta wannan

Tinubu ya samu sauƙi a bukatar da ƴan ƙwadago suka gabatar kan mafi ƙarancin albashi

Rubutun da aka wallafa a ranar 5 ga watan Mayun 2024, ya samu sama da martani 8,700, sharhi 2,000, da alamar so fiye da 100 ya zuwa ranar Alhamis, 30 ga watan Mayun 2024.

Batun tallafin Tinubu na N250,000 ga 'yan Najeriya
An binciko gaskiya kan batun Tinubu zai ba 'yan Najeriya tallafin N250,000 Hoto: Sean Gallup, Bloomberg
Asali: Getty Images

Yawancin masu sharhi kan rubutun sun nuna sun ji daɗin hakan, wanda hakan ya sa wani dandalin duba gaskiya, Dubawa, ya binciki iƙirarin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Menene gaskiya kan tallafin gwamnatin Tinubu?

Dandalin ya ce ya bi adireshin yanar gizon da aka sanya a cikin rubutun kuma bai samu wani abu ciki da ya nuna a yi rajista ko cancantar samun tallafin gwamnatin tarayya ba.

Maimakon haka, shafin yanar gizon na TGuideWeb ya nuna yadda ƴan Najeriya za su iya samu a ɗauki nauyin bizarsu zuwa ƙasar Amurka.

Dandalin binciken ya kammala da cewa:

"Adireshin yanar gizon da aka sanya a cikin rubutun bai nuna wani shirin tallafi mallakin gwamnatin tarayya ba."

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta dawo da shirin rage talauci ga 'yan Najeriya miliyan 75

"Bugu da ƙari masu zamba suna amfani da bayanan da ke cikin irin waɗannan shafukan yanar gizon wajen yin munanan ayyuka.
"Saboda haka ya kamata mutane su yi hattara da shafin yanar gizon na bogi."

Tinubu ya dawo da shirin tallafi

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin tarayya ƙarƙashon jagorancin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ta dawo da shirin bayar da tallafi ga ƴan Najeriya.

Shirin bayar da tallafin kuɗin zai amfani mutane miliyan 75 a cikin gidaje miliyan 50 domin rage musu raɗaɗin talauci da suke fama da shi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng