Duk da Umarnin Kotu da ke Neman Sauke Sanusi II, Mataimakin Gwamna Ya Gana da Sarki

Duk da Umarnin Kotu da ke Neman Sauke Sanusi II, Mataimakin Gwamna Ya Gana da Sarki

  • Mataimakin gwamnan jihar Kano, Abdulsalam Aminu Gwarzo ya kai ziyara fadar mai martaba Muhammadu Sanusi II a fadarsa
  • Gwarzo ya kai ziyarar a ranar Laraba 29 ga watan Mayu duk da umarnin Babbar Kotun Tarayya kan kujerar Sanusi II a yanzu
  • Wannan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da dmabarwa kan sarautar jihar Kano da ya ki ci ya ki cinyewa tun a makon jiya

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Yayin da ake cigaba da dambarwa kan masarautun Kano, mataimakin gwamna jihar, Aminu Abdussalam Gwarzo ya ziyarci Muhammadu Sanusi II.

Gwarzo ya kai ziyarar duk da umarnin Babbar Kotun jiha kan tuge sabon sarkin daga karagar sarauta a jihar.

Kara karanta wannan

Wa zai zama Sarkin Kano? Abin da kotuna 2 suka ce game da makomar Sanusi II da Aminu

Duk da matsin sa Sanusi II ke ciki, Gwarzo ya samu ganawa da shi a fadarsa
Abdulsalam Aminu Gwarzo ya gana da Muhammadu Sanusi II a fadarsa. Hoto: @HonAbdullahiM12.
Asali: Twitter

Kano: Gwarzo ya gana da Sanusi II

A cikin faifan bidiyon da aka yada a shafin X, an gano Gwarzo da tawagarsa suna shiga cikin fadar a yau Laraba 29 ga watan Mayu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai babu karin bayani kan abin da suka tattauna amma hakan bai rasa nasaba da yin mubaya'a ko goyon baya ga Sarkin.

Ba wannan ne karon farko da mataimakin gwamna ya ziyarci fadar sarkin Kano ba.

Musabbabin rikicin sarautar Kano

An shiga rikicin sarauta a Kano tun bayan tube sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero daga kan karaga.

Gwamnan Abba Kabir Yusuf ya sauke Aminu Ado bayan sanya hannu a sabuwar dokar Majalisar jihar.

A makon da ya gabata ne Majalisar ta amince da rushe masarautu guda biyar da gwamnan Abdullahi Ganduje ta kirkiro a shekarar 2019.

Kara karanta wannan

Ana tsaka da ruɗanin hukuncin kotuna 2, jigon NNPP ya yi magana kan naɗin Sarkin Kano

Lauya ya magantu kan rikicin sarautar Kano

A wani labarin, an ji wani lauya a Najeriya, Wale Adeagbo ya yi martani kan rikicin sarautar jihar Kano da ke faruwa a yanzu.

Lauyan ya koka kan yadda kotuna ke ba da umarni masu cin karo da juna kan matsalar sarautar jihar.

Sai dai ya ce a tsarin doka babu inda aka tabbatar cewa Babbar Kotun Tarayya ta fi Babbar Kotun jiha iko.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel