Dawo da Tsohon Taken Najeriya Ya Fusata Jama’a, Ana Zafafan Martani ga Bola Tinubu

Dawo da Tsohon Taken Najeriya Ya Fusata Jama’a, Ana Zafafan Martani ga Bola Tinubu

  • A yau ne shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya kaddamar da sabon taken Najeriya da za a cigaba da amfani da shi a kasar
  • Sai dai a bisa dukkan alamu sabon taken ya fusata yan kasa musamman yadda aka samar da dokar a kankanin lokaci
  • Legit ta tatttaro muku ra'ayoyin daban-daban da yan Najeriya suka bayyana a kafafen sada zumunta kan sabon taken kasar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya kaddamar da sabon taken Najeriya a yau Laraba, 29 ga watan Mayu.

Sai dai taken bai samu karbuwa yadda ya kamata ba a wajen yan kasa musamman lura da halin da kasar ke ciki.

Kara karanta wannan

Taken Najeriya: Hadimin tsohon shugaban kasa ya caccaki Tinubu a karon farko

Bola Tinubu
An caccaki Tinubu kan dawo da tsohon taken Najeriya. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
Asali: Facebook

'Yan Najeriya da dama sun bayyana ra'ayoyin nuna kin amincewa da sabon taken kamar yadda jaridar Daily Trust ta tattaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sabon take: Martanin yan Najeriya:

Ko taken zai yi maganin yunwa?

A cikin shaguɓe wani mai amfani da kafar X, @Zarmaomar yake tambaya ko sabon taken zai iya magance yunwa a Najeriya?

Cikin shaguɓe ya kara da cewa ko sabon taken zai magance matsalolin tsaro, cin hanci da samar da ayyuka a Najeriya?

An kara zama bayin turawa

Wata mai amfani da kafar X, @RealQueenBee_ ta ce maido da tsohon taken ya nuna cewa Najeriya ta koma bauta ga turawa.

Ta fadi haka ne kasancewar sabon taken turawan mulkin mallaka ne suka kirkiro shi kuma Najeriya ta yi amfani da shi a baya.

'Idan ana yunwa ba a magana'

Wani mai amfani da kafar X, @PatoEner ya ce ya kamata gwamnati ta kirkiro tsare-tsaren da za su rage wahalar da ake ciki ne a halin yanzu.

Kara karanta wannan

Jerin alkawuran da Shugaba Bola Tinubu ya gagara cikawa cikin shakara 1

Domin a cewarsa, idan al'umma na cikin yunwa mutane ba za su ma iya rera sabon taken ba saboda hankalinsu zai koma kan abinci.

Ko sabon taken zai sauke farashi?

Wata mai amfani da kafar X, @iam_damayor ta yi gatse wajen taya ƴan Najeriya murnar samun sabon take. Ga abin da take cewa:

"Na muku murnar samun sabon take. Idan za ku je sayayya kasuwa, sai ku karanta sabon taken domin a sayar muku kaya a farashin shekarar 2015."

Wandanda suka taimaki Tinubu a 2023

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya cika shekara da ɗarewa mulkin Najeriya bayan ya gaji Muhammadu Buhari.

Mai girma Bola Tinubu ya bayyana wadanda suka masa sharar fage har ya samu damar zama zaɓaɓɓen shugaban kasa a Najeriya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Online view pixel