Wani Kasurgumin Ɗan Bindiga da Ya Addabi Mutane Ya Miƙa Wuya Ga Sojoji a Kaduna

Wani Kasurgumin Ɗan Bindiga da Ya Addabi Mutane Ya Miƙa Wuya Ga Sojoji a Kaduna

  • Wani hatsabibin ɗan bindiga, Lawal Kwalba ya miƙa wuya ga rundunar sojojin Najeriya a Kaduna ranar Talata, 28 ga watan Mayu
  • A wata sanarwa da rundunar sojin ta fitar, ta ce tubabben ɗan ta'addan ya mika makamai da kayan aikinsa ga dakarun sojoji
  • Ta ce wannan wata alama ce da ke nuna hare-haren da jami'an tsaro ke kai wa maɓoyar yan ta'adda ya matsa masu lamba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kaduna - Wani ƙasurgumin kwamandan ƴan bindiga, Lawal Kwalba ya miƙa wuya ga rundunar sojojin Najeriya a jihar Kaduna.

Rundunar sojojin ƙasa ta Najeriya ce ta bayyana haka a wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na manhajar X wanda aka fi sani da Twitter yau Laraba.

Kara karanta wannan

Luguden wutan sojojin sama ya soye 'yan ta'adda a jihohin Katsina da Borno

Sojojin Najeriya.
Kwamandan yan bindiga Lawal Kwalba ya tuba ya mika wuya ga sojoji a Kaduna Hoto: Nigeria Army
Asali: Twitter

Sanarwar ta ce wannan na zuwa ne yayin da dakarun sojoji ke ci gaba matsa wa ƴan ta'adda da nufin kawo karshen duk wani nau'in ta'addanci a ƙasar nan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rundunar ta ce kwamandan ƴan bindigan ya miƙa kansa ranar Talata 28 ga watan Mayu, 2024 biyo bayan zafafan hare-haren da sojoji ke kai wa mafakar ƴan bindiga a Kaduna.

Sojoji sun zafafa kai hare-hare

A cewar sanarwar, babu ko shakka hare-haren da sojoji ke kai wa maɓoyar ƴan ta'adda daban-daban sun hana su sakat, wanda bisa haka ne Kwalba ya zaɓi miƙa wuya.

Wani sashen sanarwar ta ce:

"Wannan miƙa wuya ya nuna irin nasarorin da sojoji ke samu a yaƙi da ƴan ta'adda a jihar Kaduna da kewaye.
"Bayan ya miƙa wuya, sojojin sun karɓi bindigogi kirar AK-47 guda biyu, babur daya, da Magazine biyu dauke da harsasai na musamman daga hannun dan ta'addan."

Kara karanta wannan

Wani shugaban ƴan bindiga ya gamu da ajalinsa yayin da suka kai hari a Katsina

A halin yanzu dai Kwalba na hannun sojoji a ɗaya daga cikin sansanonin su kuma ana sa ran za a samu muhimman bayanai da za su taimaka wajen kakkaɓe sauran ƴan ta'adda.

Rundunar sojojin ta tabbatar da cewa dakaru za su ci gaba da aiki ba dare ba rana domin dawo da zaman lafiya da tsaro a Kaduna da yankin baki ɗaya.

ISWAP ta kashe masunta a Borno

A wani rahoton kuma ƴan ta'adda ɗauke da makamai na ƙungiyar ta'addanci ta ISWAP sun kao hari kan masunta a ƙaramar hukumar Kukawa ta jihar Borno.

Miyagun ƴan ta'addan sun hallaka masunta mutum 15 lokacin da suke shirin fara kun kifi da daddare a ranar Lahadi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel