'Abin Kunya': NBA Ta Soki Lauyoyi da Masu Shari'a Kan Dambarwar Masarautar Kano

'Abin Kunya': NBA Ta Soki Lauyoyi da Masu Shari'a Kan Dambarwar Masarautar Kano

  • Kungiyar lauyoyi ta kasa NBA ta bayyana yadda ake samun hukunce-hukunce masu karo da juna daga kotunan Kano a matsayin abin kunya ga bangaren shari'a
  • Shugaban kungiyar, Yakubu Maikyau, OON, SAN ta cikin sanarwa mai dauke da sa hannun sakataren yada labaran kungiyar, Akorede Lawal ya ce an yi illa ga shari'a
  • Shugaban ya kara da cewa alkalan da dambarwar masaurautar ta rutsa da su su gaggauta duba yadda suke gudanar da aikinsu domin ceto mutuncin shari'a a Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano- Shugaban kungiyar lauyoyi ya kasa (NBA) Yakubu Maikyau, OON, SAN ya bayyana yadda ake ta wasa da hukuncin kotu kan dambarwar masarautar Kano abin kunya ne matuka.

Kara karanta wannan

Sarautar Kano: Lauya ya feɗe gaskiya, ya nemowa Aminu Ado da Sanusi II mafita

A cikin wata sanarwa da ya fitar, ya nuna takaicin yadda kotun tarayya ta yanke hukunci, sannan babbar kotun jiha ta yanke wani hukuncin, aka kuma komawa ga babbar kotun tarayya ta kara zartar da wani hukuncin.

Masaurata
NBA ta bayyana takaicin hukunce-hukunce kan dambarwar masarautar Kano Hoto: HRH ALH DR. AMINU ADO BAYERO CFR, EMIR OF KANO, Y. C Maikyau, SAN, FCIArb UK, Muhammadu Sanusi II
Asali: Facebook

Channels Television ta wallafa cewa sanarwar mai dauke da sa hannun sakataren yada labaran NBA, Akorede Lawal ta ce yadda aka rika yanke hukuncin cin fuska ne ga bangaren shari’a.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'An yi illa ga sashen shari'a a Kano'

Kungiyar lauyoyi ta kasa (NBA) ta ce hukunce-hukunce masu karo da juna da kotuna suka fitar kan rikicin sarautar Kano ya yi illa babba ga bangaren shari'a a kasar nan.

The Nation ta wallafa cewa shugaban kungiyar, Yakubu Maikyau, OON, SAN na ganin za a dade kafin a farfado daga illar ganin yadda alkalai da lauyoyin suka gudanar da aikinsu a dambarwar masarautar Kano.

Kara karanta wannan

Jam’iyyun siyasa sun yi kewar Buhari, ana Allah wadai da shekarar farko a mulkin Tinubu

Ya umarci alkalan da suka rika yanke hukunce-hukuncen su gaggauta waiwayar yadda suka gudanar da aikinsu da zimmar kawo gyara domin ceto mutuncin shari'a, inda ya ce za a kuma hukunta wadanda suka saba dokar aiki.

An haramta zanga-zanga a Kano

A baya mun kawo muku labarin cewa gwamnatin jihar Kano ta haramta zanga-zanga kowace iri a fadin jihar domin gujewa tayar da hankulan al'umma.

Darakta janar na gwamna Abba Kabir Yusuf kan yada labarai, Sunusi Bature Dawakin Tofa ne ya fitar da sanarwar da safiyar Laraba, inda ya ce matakin ya zama dole.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.