Jam’iyyun Siyasa Sun Yi Kewar Buhari, Ana Allah Wadai da Shekarar Farko a Mulkin Tinubu

Jam’iyyun Siyasa Sun Yi Kewar Buhari, Ana Allah Wadai da Shekarar Farko a Mulkin Tinubu

  • Kungiyar gamayyar jam'iyyun siyasa (CUPP) ta kushe gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu cikin shekara daya da ya yi
  • Kakakin kungiyar ya ce yan Najeriya sun sa ran samun sauki amma reshe ya juya da mujiya, wahala kawai suke sha ta kowanne fanni
  • Har ila yau kakakin ya bayyana yadda tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fi Tinubu kokarin gudanar da mulki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Nigeria - Kungiyar gamayyar jam'iyyun siyasa (CUPP) ta caccaki gwamnatin shugaba Bola Tinubu kan rashin iya gudanar da mulki.

Shugaba Bola Tinubu
Kungiyar CUPP ta cakkaki Tinubu bayan cika shekara kan mulki. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa kungiyar ta fitar da bayani kan gwamnatin Bola Tinubu ne domin auna kokarin da ya yi bayan shekara kan karaga.

Kara karanta wannan

Tinubu ya kinkimo namijin aikin da zai amfani mutane miliyan 30 a Najeriya

Kakakin kungiyar, Kwamared Mark Adebayo ne ya yi jawabin ga manema labarai a ranar Talata, 27 ga watan Mayu 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsammanin 'yan Najeriya ga Bola Tinubu

Kungiyar CUPP ta ce yan Najeriya sun kyautata wa Tinubu zato kan cewa zai share musu hawaye amma sai ya kara jefa su cikin wahala.

Yadda Tinubu ya rika tutiyar kwarewa da iya shugabanci an yi tsammanin samun haɓakar tattalin arziki, samun tsaro da cigaban ilimi amma hakan ya gagara.

Tinubu da Buhari: wa ya fi kokari?

Kungiyar CUPP ta ce ba ta yi tsammanin za a samu shugaba da zai yi kasa da abin da Muhammadu Buhari ya yi ba.

Amma sai ga shi cikin shekara daya Bola Tinubu ya kawo tsaruka da ya nuna yafi Muhammadu Buhari gazawa a kan gudanar da mulki.

CUPP: Yadda Tinubu ya gasa talakawa

Kara karanta wannan

Ranar yara: Tinubu ya yi alkawura kan inganta rayuwar kananan yara

Har ila ila yau kungiyar CUPP ta ce ba a taba samun shugaban da ya gasawa talakawa aya a hannu ba kamar Bola Tinubu.

Ta ce abin bakin ciki ne a ce ranar da Tinubu ya karbi mulki talakawa suka fara dandana kudarsu a hannunsa saboda cire tallafin mai.

Tinubu: Kungiyar Arewa ta bada hakuri

A wani rahoton, kun ji cewa wata kungiya mai goyon bayan shugaba Bola Ahmed Tinubu ta yi jawabi kan cikar shugaban kasa shekara daya bisa mulki.

Kungiyar ta bayyana irin kokarin da gwamnatin Bola Tinubu ta yi cikin shekara guda da kuma abin da ya kamata yan Najeriya su yi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng