Kano: Kotu Ta Umarci a Fitar da Muhammadu Sanusi II Daga Fadar Sarki

Kano: Kotu Ta Umarci a Fitar da Muhammadu Sanusi II Daga Fadar Sarki

  • Babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kano ta ba umarnin fitar da Muhammadu Sanusi II daga fadar Sarkin Kano da ke Gidan Rumfa
  • Kotun ta kuma hana waɗanda ake ƙara daga gayyata, kamu ko muzgunawa Sarkin Kano na, Mai martaba 15 Aminu Ado Bayero
  • Alƙalin kotun mai shari'a S. A Amobeda wanda ya ba da umarnin ya ce ya yi hakan ne domin adalci da wanzar da zaman lafiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kano ta bayar da umarnin korar Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II daga fadar Sarkin Kano ta Gidan Rumfa.

Kotun ta kuma umarci ƴan sanda da su tabbatar an dawo da duk wani haƙƙi da alfarmar da Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero yake da su.

Kara karanta wannan

Ana tsaka da ruɗanin hukuncin kotuna 2, jigon NNPP ya yi magana kan naɗin Sarkin Kano

Kotu ta umarci a fitar da Sanusi II daga fadar Sarkin Kano
Kotu ta umarci a fitar da Muhammadu Sanusi II daga fadar Sarkin Kano @Abdullahiabba_, @Imranmuhdz
Asali: Twitter

Ana ta faman rikici kan sarautar Kano

An tsige Aminu Ado Bayero ne a makon da ya gabata bayan amincewa da gyaran da aka yiwa dokar masarautun jihar Kano.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayan an amince da kuɗirin dokar da majalisar dokokin jihar tayi, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya rattaɓa hannu kan ƙudirin.

Alƙalin kotun, mai shari’a S. A. Amobeda, wanda ya bayar da umarnin a ranar Talata ya bayyana cewa ya ba da umarnin ne domin tabbatar da adalci da wanzar da zaman lafiya a Kano, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

Sarki: Wane umarni kotun ta ba da?

Kotun ta ba da umarnin wucin gadi na hana waɗanda ake ƙara ko wakilansu daga gayyyata, kamu, tsarewa ko muzgunawa wanda ya shigar da ƙarar har zuwa lokacin da za ta yanke hukunci kan shari'ar, rahoton The Nation ya tabbatar.

Kara karanta wannan

Sanusi II: Kotu ta ba jami'an tsaro sabon umarni kan Sarkin Kano

Kotun ta kuma ba da umarnin haramta waɗanda ake ƙara daga hana Aminu Ado Bayero yin amfani da gidansa da fadar Sarki da ke Kofar Kudu da cin gajiyar duk wani ƴanci da yake da shi na zama Sarkin Kano.

Kotun ta kuma hana fitar da wani abu ko wani mutum daga fadar har zuwa lokacin da za ta yanke hukunci kan ƙarar.

An ɗage ƙarar zuwa ranar 4 ga watan Yunin 2024 domin fara sauraronta.

Kotu ta hana fitar Sanusi II daga fada

A wani labarin kuma, kun ji cewa wata babbar kotu a jihar Kano ta hana jami'an tsaro fitar da Muhammadu Sanusi II daga cikin fadar Sarkin Kano.

Kotun ta kuma hana jami'an tsaro na ƴan sanda, sojoji da DSS daga gayyata, kamu, muzgunawa ko yin katsalandan kan ayyukan Sarkin Kano na 16.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel