Sanusi II: Kotu Ta Ba Jami'an Tsaro Sabon Umarni Kan Sarkin Kano

Sanusi II: Kotu Ta Ba Jami'an Tsaro Sabon Umarni Kan Sarkin Kano

  • Wata babbar kotun jihar Kano ta ba da umarnin wucin gadi kan ƙarar da Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II da masu naɗin Sarkin suka shigar
  • Kotun ta hana jami'an tsaro na ƴan sanda, sojoji da jami'an hukumar ƴan sandan farin kaya fitar da Muhammadu Sanusi II daga cikin fadar Sarki
  • Kotun ta kuma hana jami'an tsaron yin katsalandan kan ayyukan Muhammadu Sanusi II har zuwa lokacin da za ta yanke hukunci kan ƙarar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Wata babbar kotu a jihar Kano ta ba ƴan sanda, hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) da sojojin Najeriya sabon umarni kan Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II.

Kotun ƙarƙashin jagorancin mai shari'a Amina Aliyu ta hana hukumomin tsaron fitar da Muhammadu Sanusi II daga fadar Sarkin Kano.

Kara karanta wannan

Ana tsaka da ruɗanin hukuncin kotuna 2, jigon NNPP ya yi magana kan naɗin Sarkin Kano

Kotu ta hana fitar da Sanusi II daga fadar Sarkin Kano
Kotu ta hana jami'an tsaro fitar da Sanusi II daga fadar Sarkin Kano Hoto: Nigeria Police Force, Sanusi Lamido Sanusi, DSS
Asali: Facebook

Sarkin ya shigar da ƙarar ne tare da masu naɗa Sarkin Kano mutum huɗu da suka haɗa da Madakin Kano, Yusuf Nabahani, Makaman Kano Ibrahim Sarki Abdullahi, Sarkin Bai, Mansur Adnan da Sarkin Dawaki Maituta, Bello Tuta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wane umarni kotun ta ba da kan Sanusi II?

Da take bayar da wannan umarnin, Mai shari’a Amina Aliyu ta kuma hana jami’an tsaro kamawa ko muzgunawa Sarkin da masu naɗa Sarkin, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

Kotun ta kuma ba da umarnin wucin gadi na hana waɗanda ake ƙara ko wakilansu daga muzgunawa, gayyata ko cafke masu shigar da ƙarar har sai ta yanke hukunci kan shari'ar, rahoton Daily Nigerian ya tabbatar.

Kotun ta kuma hana waɗanda ake ƙara yin katsalandan kan ayyukan Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II har zuwa lokacin da za ta yanke hukunci kan ƙarar.

Kara karanta wannan

Kano: Kotu ta umarci a fitar da Muhammadu Sanusi II Daga Fadar Sarki

Daga nan sai mai shari'a Amina Aliyu ta ɗage ƙarar zuwa ranar 13 ga watan Yunin 2024 domin fara sauraronta.

Batun tsige Sarki Sanusi II a Kano

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙungiyar lauyoyin Arewacin Najeriya sun ba gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf wa'adin awa 48 ya janye naɗin da ya yi wa Sarki Muhammadu Sanusi II.

Lauyoyin, waɗanda suka bayyana kan su a matsayin 'ƙungiyar lauyoyin Arewa', sun ba da wa’adin ne a wani taron manema labarai a birnin tarayya Abuja.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel