"Mun Shirya Tsaf," 'Yan Sanda Sun Kara Ɗaukar Mataki Kan Rigimar Sarautar Kano

"Mun Shirya Tsaf," 'Yan Sanda Sun Kara Ɗaukar Mataki Kan Rigimar Sarautar Kano

  • Ƴan sanda sun shirya ɗaukar matakai masu tsauri kan duk wanda ya yi ƙoƙarin tayar da fitina a jihar Kano yayin da ake taƙaddamar sarauta
  • CP Usaini Gumel, kwamshinan ƴan sandan jihar ya ce ba za su lamunci wasu tsiraru su ruguza zaman lafiyar da ake da ita a Kano ba
  • Ya kuma gargaɗi masu shirin ɗauko hayar ƴan daba daga wasu jihohi su canza tunani tun kafin lokaci ya kure masu

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kano - Rundunar ƴan sanda ta tabbatar wa al'ummar jihar Kano cewa za ta samar da isasshen tsaro yayin da ake ci gaba da taƙaddama kan sarautar sarkin Kano.

Kwamishinan ƴan sandan jihar, CP Mohammed Usaini Gumel ne ya bayyana haka yayin hira da hukumar dillancin labarai ta ƙasa (NAN) ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Aminu Ado: Dalilin kotu na umartar jami'an tsaro su fitar da Sarkin Kano na 15 daga fada

Kwamishinan yan sandan Kano, CP Gumel.
Yan sanda sun ɗauki matakin tabbatar da tsaro a Kano Hoto: Kano Police Command
Asali: Facebook

Ya ce jami'an ƴan sanda sun shirya tunkarar duk wani mutum ko tawaga da ka iya yunkurin tayar da tarzoma a kowane lungu da saƙo na jihar, The Nation ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A kalamansa ya ce:

"A shirye muke mu tunkari duk wani mutum ko gungun mutanen da suka yi yunƙurin wargaza mana yanayin zaman lafiya da aka san jiharmu da shi.
"Ba zamu ɗaga wa kowa ƙafa ba, mun shirya tsaf domin tabbatar da tsaro a yankin da ke ƙarƙashin kulawar mu."

'Yan sanda sun gargaɗi mutanen Kano

CP Gumel ya kuma gargadi mutanen da ke da niyyar shigo da ‘yan baranda zuwa Kano daga wasu sassan kasar nan da su canza tunani tun lokaci bai ƙure masu ba.

A cewarsa, dakarun ƴan sanda za su ɗauki tsauraran matakan tsaro domin magance ko wace irin barazana a jihar Kano.

Kara karanta wannan

Rikicin masarauta: 'Yan sanda sun bankado shirin tada tarzoma a Kano, sun yi gargadi

Ya tunatar da jama’a cewa kundin tsarin mulkin Najeriya ya fito karara game da alhakin da ya rataya a wuyan ‘yan sanda wajen samar da tsaron cikin gida a Nijeriya.

“Rundunar ‘yan sanda ba za ta lamunci duk wani abu da zai haifar da rikici ko tashin hankali a jihar Kano ba."
“Mun baza jami’an tsaro isassu domin kamo duk wanda ya yi yunkurin kawo cikas ga zaman lafiya ko karya doka a jihar,”

- Useini Gumel.

Ƴan sanda sun haramta yawo da makami

Gumel ya tunatar da mazauna jihar cewa babu wanda aka ba izinin yawo da makami a kusa da fadar Sarki da gidan sarki da ke Nasarawa.

Kwamishinan ya kuma roƙi al'umma da su taimakawa ƴan sanda da bayanai domin kai ɗauki kan duk wani abu da iya tayar da fitina, Daily Post ta ruwaito.

Sarki Aminu Ado ya faɗa matsala

A wani rahoton kuma, babbar kotun jiha ta bayar da umarni uku kan sarkin Kano na 15 da sauran sarakuna huɗu da Abdullahi Ganduje ya naɗa.

Kara karanta wannan

Sanusi II vs Aminu Ado: Atiku ya yi magana kan rikicin sarautar Kano, ya fadi mai laifi

A wata hira da mai magana da yawun kotunnan jihar, ya bayyana abin da ya sa kotun ta ɗauki wannan mataki a ƙarar da aka shigar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262