Masarautu: 'Karya ne' Gwamnati ta yi Martani Kan Rahoton Tashin Hankali Kano

Masarautu: 'Karya ne' Gwamnati ta yi Martani Kan Rahoton Tashin Hankali Kano

  • Gwamnatin jihar Kano ta musanta rahoton bullar tashin hankali na nuna rashin goyon bayan rushe masarautu da tsige sarakuna guda biyar
  • Wannan na zuwa ne bayan rahotanni sun ce wasu matasa sun bazama titunan Kano suna zanga-zangar da ta daga hankalin jama'a
  • Kwamishinan yada labaran jihar, Baba Halilu Dantiye ya tabbatar da cewa wasu tsagerun matasa sun taru, amma tuni aka dakile aniyarsu na rigima

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano- Gwamnatin jihar Kano ta yi martani kan labarin dake bayyana bullar tashin hankali a jihar saboda rushe masarautu da nada sabon sarki.

A wata sanarwa da kwamishinan yada labarai na jihar, Baba Halilu Dantiye ya fitar a ranar Litinin, ya ce babu kamshin gaskiya cikin labarin.

Kara karanta wannan

Rikicin Kano: Abin da Sarki Sanusi II ya faɗawa manyan jami'an tsaro a fadarsa

Abba Kabir Yusuf
Gwamnatin Kano ta musanta bullar tashin hankali saboda rushe masarautu Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Vanguard News ta wallafa cewa kwamishinan ya ce wasu 'yan daba sun dan taru, amma tuni aka tarwatsa su wanda ya dakile aniyarsu ta tada zaune tsaye.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya tabbatar da cewa Kano na zaune cikin kwanciyar hankali, kuma kowa na harkokinsa cikin lumana ba tare rashin tsoron komai ba.

Gwamnatin Kano ta ba da tabbacin tsaro

Kwamishinan yada labarai na Kano, Baba Halilu Dantiye ya ce mazauna Kano jihar su kwantar da hankalinsu yayin da aka ja daga tsakaninta da sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero.

Blueprint Newspaper ta wallafa cewa gwamnatin ta yi alkawarin cewa tana yin iya kokarinta wajen tabbatar da tsaron dukiyoyi da rayukan jama'a.

Wannan na zuwa ne bayan bullar rahoton rikici a jihar na nuna rashin goyon bayan rushe masarautu da tsige sarakuna tare da nadin Malam Muhammadu Sanusi II.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta tona waɗanda suka shirya zanga zanga kan rusa masarauta

Kwamishinan ya bayyana cewa babu wani dalili da zai sa mutane su daga hankulansu, domin komai na tafiya cikin lumana.

Kano: 'Yan Sanda sun gano shirin tarzoma

Mun ba ku labarin cewa rundunar 'yan sandan Kano ta bankado shirin tayar da hankalin mazauna jihar da sigar nuna rashin goyon bayan rushe masarautu.

Kwamishinan 'yan sandan jihar, CP Muhammed Usaini Gumel ne ya bayyana haka, inda ya ce sun gano tsagerun na shirin kai hari a muhimman wurare.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.