Gwamnatin Kano Ta Tona Waɗanda Suka Shirya Zanga Zanga Kan Rusa Masarauta

Gwamnatin Kano Ta Tona Waɗanda Suka Shirya Zanga Zanga Kan Rusa Masarauta

  • Gwamnatin Kano ta yi bayani biyo bayan zanga zanga da ake samu bayan rusa masarautun jihar da dawo da Sanusi II
  • A sanarwar da gwamnatin ta fitar ta ce dawo da Muhammadu Sanusi II kan mulki shi ne ra'ayin al'ummar jihar Kano
  • Har ila yau, gwamantin ta bayyana dalilan da ya sa ta yi wannan jawabi a yayin da wasu ke kone-kone kan rusa masarautun

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Gwamnatin jihar Kano ta yi karin haske kan rusa masarautun da gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi a makon da ya wuce.

Abba sanusi gaya
Gwamnati ta zargi yan siyasa da neman tayar da rikici a Kano. Hoto: Abba Kabir Yusuf|Masarautar Kano
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa gwamnatin ta ce rusa masarautun shi ne abin da mutanen Kano ke bukata a yanzu.

Kara karanta wannan

Masarautu: 'Karya ne' Gwamnati ta yi martani kan rahoton tashin hankali Kano

Kwamishinan yada labarai na jihar, Baba Halilu Dantiye ne ya bayyana lamarin ga manema labarai a yau Litinin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rusa masarautu ya jawo rikici a Kano?

Kwamishinan yada labaran jihar Kano ya ce rusa masarautun jihar da gwamna Abba Yusuf ya yi bai kawo tashin hankali ba.

Ya bayyana haka ne a matsayin martani ga masu yada bidiyo a kafafen sadarwa suna nuna cewa ana tashin hankali a jihar Kano saboda sauke Aminu Ado Bayero.

Kwamishina: "Ba a cikin fargaba a Kano"

A cewar kwamishinan, a mafi yawan sassan Kano mutane na zaune lafiya cikin aminci ba tare da wata fargaba ba.

Saboda haka ya ce wannan na nuna mafi yawan mutanen jihar sun goyi bayan rusa masarautun da kuma dawo da Muhammadu Sanusi II.

Gwamanti za ta tabbatar da zaman lafiya

Kwamishinan ya kara da cewa kananan kone-kone da zanga-zanga da ake samu a wasu wurare kadan yawanci sojojin haya ne da aka ɗauka suke yi.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta nemi alfarma wajen Tinubu kan Aminu Ado Bayero

Amma duk da haka ya ce gwamnati za ta tabbatar da cewa kowa na zaune lafiya a cikin Kano kuma ba za ta bar wutar da karu ba.

An yi zanga zanga a Kano

A wani rahoton, kun ji cewa kwanaki kadan da tsige sarakuna biyar na masarautun Kano, zanga-zanga ta barke a karamar hukumar Gaya domin nuna adawa ga gwamnati.

Masu zanga-zangar sun nuna bakin cikinsu kan rusa masarautun suna masu yin zargin cewa matakin na da alaka da siyasa ne kawai.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng